Mutane 5 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Harbe-Harben da Kai a Jahar Cross River

 

Harbe-harbe sun tsananta a daren Talata a wasu unguwanni biyu na wurin Yala dake jahar Cross River.

Kamar yadda rohotanni suka tabbatar, an ga gawar mutane 5 da kuma har yanzu harbe-harben basu tsaya ba.

Kwamishinan ‘yan sandar jahar ya tabbatar da aika jami’ansa yankin don kwantar da tarzomar.

Yala, Cross River – Da daren Talata ne aka fara jin harbe-harbe ko ta ina a wasu unguwanni biyu dake wuraren Yala a jahar Cross River.

Anji harbin ne a O’oba da Okpame tun cikin dare har yanzu haka ba a daina ji ba kamar yadda wakilin Daily Trust na jahar yace.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar ya dauka mataki

Kwamishinan ‘yan sanda na Cross River ya tabbatar da tura jami’ansa da yayi yankin don kwantar da tarzoma.

Wasu bata-gari daga O’Oba sun afka wasu anguwannin suna harbe-harbe, a cewarsa.

Ina sane da abubuwan da suke faruwa don haka ne yasa na tura yarana yankin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai gidajen da aka bankawa wuta. Daya daga cikin gidajen na Gabe Onah ne, tsohon shugaban CRCC.

Yanzu haka ba a riga an tantance yawan asarorin da aka tafka ba. Amma an tsinci gawar mutane 5 da aka harbe har lahira.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here