Matsalar da Zata sa Kudu Maso Gabashin Najeriya ta Rasa Takarar Shugaban Kasa a 2023 – Adeseye Ogunlewe

 

Wani tsohon minista ya bayyana rashin hadin kan mutanen kudu maso gabas a matsayin matsalarsu.

Ya bayyana cewa, suna da kudi, kuma sun watsu a kowane sashe na Najeriya, amma basu da hadin kai.

Ya kuma bayyana cewa, babu wanda ya fi cancantar gadon kujerar shugaba Buhari a 2023 fiye da Bola Tinubu.

Wani tsohon Ministan Ayyuka a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya ce Kudu maso Gabas ba za su iya samar da shugaban kasar Najeriya na gaba ba saboda ba su da hadin kai.

Ya fadi hakan ne yayin wani shirin Arise TV mai suna ‘The Morning Show’ a ranar Laraba 11 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

A cewarsa, babu wani dan takarar da ya fi dacewa ya jagoranci kasar nan a 2023 fiye da tsohon gwamnan jahar Legas Bola Tinubu – wata sanarwa da Bode George, memba na kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, wanda shi ma ya kasance a cikin shirin.

Ya yi ikirarin cewa rashin iya jagoranci da rashin hadin kai zai yi tasiri kan duk wani dan takarar shugaban kasa na Kudu maso Gabas.

Ya ce:

“Wasu rukunin mutane da suka dace, su ne mutanen Kudu maso Gabas amma suna da matsalar shugabanci.

“Suna da baiwar da suka bazu ko’ina a cikin Najeriya kuma suna iya samun kuri’u da yawa, amma sun basu da hadin kai kwata-kwata.

Mutumin Imo, dan Enugu, dan Ebonyi ba za su saurari kansu ba. “Suna da kudi. Idan suka zauna suka tattara abin da za su iya bayarwa, suna da kudi fiye da kusan kowa a Najeriya.

“Amma kun taba ganin mutum daya daga kudu maso gabas ya ce ‘Ina sha’awar shugabancin kasa, zan fara kamfen a duk fadin Najeriya nan da nan, ku tara mani kudi?’ Kuma ya yi tasiri ga tsarin jam’iyya?”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here