Rikicin Rasha da Ukraine: Gwamnatin Rasha ta Saki Jerin Sunayen Kasashen da ba ta ga Maciji da su
Gwamnatin Rasha ta saki jerin sunayen kasashe da yankunan da ba ta ga maciji da su yayin da ta afka wa Ukraine da yaki.
Saboda takunkumin tattalin arziki da aka saka mata, tattalin arzikin kasar Rasha ya fara shiga matsala saboda kaurace mata da aka yi.
Rasha ta kutsa cikin kasar Ukraine a watan Fabrairu, amma dakarunta sun samu tsaiko saboda matsalar zirga-zirga da turjiyya daga sojojin Ukraine.
Moscow – Rasha a ranar Litinin 7 ga watan Maris ta wallafa jerin sunayen kasashen kasar waje da ta dauke su a matsayin wadanda ta ‘ki jini’, Newsweek ta rahoto.
Rasha ta ce daga yanzu ana bukatar izini na musamman daga gwamnati kafin a yi ko wane irin kasuwanci ne da kasashen, a wani martanin da ta yi na takunkumin karya tattalin arziki da aka saka mata kan kutsa wa cikin Ukraine.
Read Also:
Jerin kasashen da Rasha ta ce bata ga-maciji da su
Kasashe da yankunan da Rasha ta dauka a matsayin makiyanta sun hada da Australia, Albania, Andorra, the United Kingdom, Anguilla, British Virgin Islands, Gibraltar, Iceland, Canada, Liechtenstein, Micronesia, Monaco, New Zealand, Norway, da Taiwan.
sai an nemi izini daga gwamnati kafin a yi kasuwanci da kasashen, Gwamnatin Rasha
Ana bukatar izini daga wata hukuma ta Gwamnatin Rasha – Hukumar Kula da Hannun Jari na Kasashen Waje, wacce aka kafa a 2008 don saka ido kan hannun jari na kasashen waje ta sanar.
Sanarwar ta ce kamfanoni, yan kasuwa da mazauna Rasha za su rika biyan bashi da ake binsu na kasashen wajen ne ta hanyar amfani da rubles.
Wannan dokar ya shafi duk wata hada-hadar kudi da za a yi da ya kai rubles miliyan 10. Sanarwar ta kuma ce hukumar na gwamnatin Rasha da ke kula da saka hannun jari ce za ta rika bada izinin yin kasuwanci da yan kasar Rasha.