Yadda Rashin Dala ya Shafi ‘Yan Najeriya

 

‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsala da shan wahala wajen canza dalar Amurka a babban bankin kasar (CBN) a kan farashin gwamnati.

Wadanda wannan lamari ya fi shafa su ne matafiya kasar waje wadanda yake daukar su lokaci kafin su samu canjin yin kasuwanci (BTA) da canjin kashewa (PTA) a sanjin gwamnati mai sauki domin zuwa asibiti ko karatu ko harkar kasuwanci.

Wannan rashi ya shafi iyaye saboda wahalar samun dala domin biyan kudaden makaratun yaransu da ba su kudin kashewa.

Bincike ya nuna cewa akwai matuƙar wahala wajen samun dala saboda bukatarta ta fi adadin da ake da ita, lamarin da ya tursasa wa bankuna ƙara tsawon lokutan samar da PTA/BTA daga makonni biyu zuwa takwas.

Amma wasu masana sun bayyana cewa CBN ta tsananta hanyar samun dalar ne saboda wasu marasa kishin kasa na amfani da tsarin ba yadda ya dace ba.

Sakamakon bincike da babban bankin ya yi ya nuna cewa akwai mutane da yawa da ba su da niyyar tafiyar kasar waje, ko amfani da kudaden a kasar waje don amfani da su akan ƙa’ida.

Amma sai su hada takardun bogi sannan su nemi banki ya ba su kudaden waje don kawai su tara, ko su sayar a kasuwannin bayan fage.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here