Jahar Kano ta Nuna Rashin Goyan Bayanta Kan Hallasta Amfani da Wiwi
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce jahar Kano bata goyon bayan hallasta amfani da ganyen wiwi a Nigeria.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban NDLEA, Buba Marwa, da jami’an hukumar suka kai masa ziyara a Kano.
Ganduje ya kara da cewa babu wani dan majalisar Kano da zai goyi bayan halasta wiwi bugu da kari musulunci ya haramta kayan maye.
Gwamna Abdullahi Ganduje na Jahar Kano, a ranar Litinin ya nuna rashin jin dadinsa kan yunkurin da ake yi na hallasta amfani da ganyen wiwi a Nigeria, The Nation ta rawaito.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai murabus) da manyan jami’an hukumar suka kai masa ziyarar ban girma a Kano.
A sanarwar da kakakin NDLEA, Mr Femi Babafemi ya fitar, ya ce gwamnan ya ce babu wani dan majalisar tarayya daga jaharsa da zai goyi bayan irin wannan yunkurin, LIB ta rawaito.
Read Also:
Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa ziyarar na NDLEA zuwa Kano na cikin shirin yakin da hukumar ke yi na ta’amulli da miyagun kwayoyi, WADA.
Ganduje ya bada tabbacin cewa gwamnatin jahar Kano bata goyon bayan sha a fataucin miyagun kwayoyi, addinin da ya fi wanzuwa a jihar na Islama shima ya hana sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Ya ce:
“Kano ce jahar mafi yawan yan majalisu a majalisar tarayya. Ina son in tabbatar maka babu wanda zai goyi bayan hallasta ganyen wiwi a cikinsu.
“Za kuma mu amince da bukatar ka na neman fili domin gina gidajen jami’an hukumar reshen jahar Kano.”
Marwa ya roki Ganduje kada ya goyi bayan halasta ganyen wiwi
Tunda farko, Marwa ya bukaci gwamnan kada ya goyi bayan duk wani yunkuri na halasta amfani da ganyen wiwi da wasu zababbun yan majalisa ke yi.
Ya ce a halin yanzu NDLEA na aiki tukuru don ganin ta takaita bazuwar haramtaciyar kwayar a Nigeria.
Ya ce halasta haramtaciyar ganyen zai janyo koma baya ga nasarar da hukumar ta samu kawo yanzu.