Rashin Jituwa ya Kunno Kai Tsakanin ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya da Shugabancin Asibitin Aminu Kano

 

Wata taƙaddama da ta taso tsakanin gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU da shugabancin asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano a Najeriyan, na barazana ga dumbin marasa lafiya a jihar Kano.

Takaddamar ta taso ne kan karin kudi a ɓangarori daban-daban da shugabancin asibitin ya yi, abin da kungiyar ta ce ba za ta saɓu ba, saboda hakan zai ƙara jefa jama’a cikin matsi.

An shiga wannan tirka-tirka ce tsakanin gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya reshen asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano sakamakon zargin cewa shugaban asibitin, ya ninka kudin asibiti, sannan JOHESU suka zarge shi da sayar da wasu bangarori na asibitin.

A baya-bayan nan cikin matakan da kungiyar ta dauka kan wannan al’amarin, har da barazanar cewa matukar lamarin ya ci gaba nan da 21 da daya ga wannan watan, to za ta shiga yajin aiki.

Wannan matakin dai ana ganin zai iya kara jefa dumbin marasa lafiya cikin kunchi.

To sai dai shugaban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Farfesa Abdurrahman Abdu Sheshe, da ke karkashin Jami’ar Bayero, ya ce batun gina wasu wurare a asibitin, ana yi ne karkashin shirin hadin gwiwar gwamnati da ‘yan kasuwa wanda gwamnatin tarayya ke ba da damar a yi.

Farfesa Abdurrhaman ya ce za su zauna da mambobin kungiyar domin tattauna yadda za a shawo kan wannan al’amari, nan gaba cikin wannan mako.

Bayanai na cewa daruruwan marasa lafiya ne ke ziyartar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano a kullum, wadanda suke cike da burin ganin an sasanta wannan takaddama don kaucewa shiga mawuyacin hali.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here