Rashin Jituwa ya Gibta Tsakanin Majalisar Wakilai da Baba Buhari
Bukatar gayyatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari gaban majalisar wakilai bai samu karbuwa ba.
A yayin zaman majalisa a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, zauren majalisar wakilan ya kaure da hayaniya yayinda yan majalisar suka sha bamban kan lamarin.
Sai dai kuma, an bukaci Shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta baci a wasu yankunan kasar.
Read Also:
Hatsaniya ya kaure a majalisar wakilai kan wani kudiri da aka gabatar na neman a gayyato Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya amsa tambayoyi a kan hauhawan rashin tsaro a kasar.
A yayin zaman majalisar a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, daya daga cikin yan majalisar ya gabatar da wata bukata na gayyatar shugaban kasar gaban majalisar dokokin tarayya.
Amma sai lamarin ya tunzura wasu yan kashenin Buhari, don haka sai rashin jituwa ya gibta a tsakani, TVC ta ruwaito.
Amma dai, bukatar neman Shugaban kasar ya kaddamar da dokar ta baci a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ya samu karbuwa a wajen yan majalisar.
Daga nan sai shugabannin majalisar suka shiga wata ganawa domin yanke hukunci kan banbancin ra’ayi da aka samu game da bukatar.