Rashin Lafiyar Umaru Musa Yar’adua: Jawabin Olusegun Obasanjo Kan Lamarin
Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana da masaniyar cewa marigayi Umaru Musa Yar’adua bashi da koshin lafiya kafin ya goyi bayansa.
Tsohon shugaban kasar ya musanta zargin cewa kutunguila da kitimurmura suka sanya shi bawa Yar’adua takara a 2007.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa yana da masaniyar cewa marigayi Umaru Musa Yar’adua bashi da koshin lafiya tun kafin ya yi masa tayin takarar kujerar shugaban kasa a 2007.
Obasanjo ya jingine manyan ‘yan siyasa da suka hada da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, da mataimakinsa a wancan lokacin, Atiku Abubakar, tare da goyawa Yar’adua baya wajen samun tikitin takara a jam’iyyar PDP.
A cewar Obasanjo, ya nemi shawarar likitoci bayan bayanai sun same shi cewa an taba yi wa marigayi Yar’adua dashen koda.
A yayin da ya ake hira da shi a wani shirin tattaunawa kai tsaye ta yanar gizo, Obasanjo ya musanta zargin cewa ya dauko marigayi Yar’adua tare da bashi takara a 2007 saboda wata bayayyiyar manufa da kutunguilar siyasa.
Read Also:
Marigayi Yar’adua ya lashe takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2007 kafin daga bisani ya rasu yana kan mulki a shekarar 2010.
“Bari na baka tarihin Umaru Yar’adua. Na san bashi da lafiya amma kafin na saka shi a gaba sai da na nemi shawarar manyan kwararrun likitoci kafin daga bisani babban abokina marigayi Farfesa Akinkugbe ya kawar min da duk shakku.
“Ya fada min cewa matukar an yi wa mutum dashen koda cikin nasara, to bashi da banbanci da sauran mutane da ke koda biyu lafiyayyu saboda guda daya ce take aiki a jikin mutum.
“Hakance ta faru akan marigayi Yar’adu, an taba yi masa dashen koda cikin nasara a baya, na san da hakan tunda sai da na nemi bayanai akan lafiyarsa.
“Ba zan manta ba ya kamu da rashin lafiya a lokacin da muke yakin neman zabe har ta kai da ya fita zuwa kasar waje domin a duba lafiyarsa, babu shi muka zo yakin neman zabe Abeokuta.
“A lokacin ne na kira shi a waya na saka a lasifika mai amsa kuwwa domin kowa na wurin taron ya ji da kunnensa a cewa Yar’adua yana nan da ransa. Nan take na tamayeshi ”Umar kana raye?’, shi kuma ya ce”ban mutu ba, ina raye”.
“Cikin ‘yan kwanaki ya dawo aka cigaba da yakin neman zabe.
“Bana jin wani mutum da ke cikin hayyacinsa zai ke zargin cewa na dauko Yar’adu da wata manufa. Na bar duk masu yi min zargin a hannun Allah”, a cewar Obasanjo.