Daga Ahmed Ibrahim

Tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960, Nijeriya ta sha fama da rikice-rikicen cikin gida da qalubalen tsaro. Tun daga juyin mulkin sojoji zuwa rikicin Maitatsine da kuma rikice-rikicen kabilanci da na addini. Nijeriya ta ga abubuwa da yawa! Abin kamar almara, da zarar wannan ana ganin an kawar da wata matasalar tsaro ko kuma an ci dunun ta, sai kuma wata ta vullo; kuma haka batun ke cigaba da kasancewa. Abu daya da ire-iren waxannan rikice-rikice ke haifarwa shi ne asarar dukiya da rayuka! Nijeriya na cigaba da fuskantar wadannan rikice-rikice wadanda ke lamushe rayukan mutane da dukiyoyinsu, dakuma tarwatsa al’ummu.

A ‘yan tsakankanin nan, dadaddiyar tsamar da ke tsakanin manoma da makiyaya musamman a shiyyar tsakiyar Nijeriya ta fadada daga abin da za a iya cewa zama wuri daya da kuma wasu dalilai da za a iya magancewa suka haifar, zuwa rikicin gangan wanda ake rura wutarsa da siyasa da addini da kuma kabilanci. Sakamakon wasu dalilai masu yawa da za a bayyana a nan gaba, wannan yanki ya zama fagen daga na rikicin manoma da makiyaya. Abin da ke daure wa mutane da yawa kai shi ne, duk da cewa rikicin makiyaya da manoma ya fi yawaita a shiyyar arewa maso yamma da arewa maso gabas, amma bai tava tsananta kamar yadda yake a arewa ta tsakiya ba; kuma ma ana yawanci dagaci ko maigari ke sasanta rikicin tun a matakin karkara ko qauyukansu. Tambayar da ta zama dole a amsa a wannan gava ita ce: Me ya sa? A bayyane take saboda muhimman dalilai biyu masu sarkakiya.

Da farko yanayin kasa da sauran batutuwan da suka hadu suka haifar da rikicin. Yankin yana da yanayin tsirrai iri biyu. Aqalla rabin yankin yana shimfide da yanayin ciyayin da ake kira Sudan Savannah, rabin kuma yanayin da ake kira Guinea Savannah a turance. Wannan ya samar da kasar noma mai kyau a yankin; da kuma ciyayi da ba sa bushewa tsawon shekara, abin da ya haifar da mafi ingancin abincin dabbobi a duk fadin kasar. A dunkule, a yayin da mazauna yankin suka rungumi ayyukan noma abinci mai yawa, su kuma Fulani makiyaya sai suka gane daukar dabbobinsu zuwa wannan yanki, musamman yankunan da suka haxu da kogin Neja da na Binuwai masu ciyayi sosai, su kuma dabbobin suna barnata kayan gona. Wannan barna a yawancin lokuta tana fusata manoman har su kashe dabbobin, inda su kuma makiyayan suke kai hare-haren daukar fansa. A dunkule, wannan ne bayanin rikicin manoma da makiyaya a Nijeriya. 

Amma duk da haka, yankin ya kasance sarke da batutuwan zamantakewa da na siyasa da rikicin manoma da makiyaya wanda ya kasance rikici a kan kasar kiwo da kasar noma da kuma wajen shan ruwa. Abu ne sananne cewa kafin mulkin mallaka babu batun rikicin kasa a Nijeriya. Akwai wadatacciyar kasar noma ga manoma da kuma kiwon dabbobi ga makiyaya. Amma sakamakon tsare-tsaren mulkin mallaka da baro karkara zuwa birane da kuma na kwanan nan, yawaitar jama’a, yankin ya yiwa makiyaya karanci. Yawancin filayen da aka ware domin amfanin makiyaya yanzu sun zama otel-otel da gidajen mai da kasuwanni da gidaje da sauransu. Duk wadannan batutuwa sun cigaba da taimakawa wajen haifar da rikicin manoma da makiyaya a yau.

Batu na biyu da yake haifar da rikicin manoma da makiyaya a shiyyar tsakiyar Nijeriya ya shafi siyasa da kabilanci da addini. Wannan ya faru tun farko, daga tsame yankin da aka yi a matsayin ‘kirkirarriyar al’umma’ wanda tsawon shekaru aka kasa samun takamammen madafar bayyana yankin. An kirkiri wannan yankin ne a karshe-karshen mulkin mallaka ne a Nijeriya. A wannan lokacin ne duk da yawan qabilu da al’adu da addinai na yankin amma ‘yan bokon yankin suka kirkiri kuma suka tilasta tarihin yankin na tsakiya. Manufar tarihin nasu shi ne bayyana cewa Jihadin Shehu Usman Danfodiyo na shekarar 1804 kaitsaye yana da alaka da mulkin mallakan Biritaniya da manufar tabbatar da Hausa Fulani sun mamaye sauran al’ummomin da ba Musulmi ba a Arewacin Nijeriya. An yi masa take da ‘Tsarin Biritaniya da Fulani’ na Marigayi Bala Takaya.

Saboda haka, wasu ‘yan yankin tsakiyan musamman karqashin jagorancin Moses Rwang sun balle daga qungiyar ‘yan kishin kasa ta tsakiyar Nijeriya don su qalubalanci abin da suka kira shirin  ‘arewantar’ da su da Sardauna Ahmadu Bello ka yi.  Su a ganin su, Sardauna yana yunkurin cigaba da abin da kakansa Shehu Usmanu Danfodiyo ya yi ne na ‘Musuluntar’ da yankin da dakushe Kiristanci. Hakan kamar yadda suka yi zato zai tabbatar da Hausa Fulani sun mamaye yankin. Wannan ya gamsar da mutanen yankin cewa suna da bambanci da Fulani makiyaya wadanda yawancinsu daga arewa maso yamma da arewa maso gabas suke, wadanda kuma suke tunanin za su mamaye al’amuran kasuwanci da siyasar yankin. Tun daga nan aka fara samun tashin-tashina, kuma ya rura wutar yanayin rikicin da wasu daga cikin batutuwan da aka tattauna a baya suka haifar.

Abin mamaki, matsalar baqi da ‘yan qasa ta zama ruwan dare a jihar Plateau; rikicin addini ya sami gindin zama a kudancin Kaduna, rikicin manoma da makiyaya ya zama batun da ke fitowa a kafafen watsa labarai daga yankin Benue, musamman a wannan zango na siyasa. An kashe sama da mutane 521, da yawa kuma sun raunata wasu sun rasa matsuguni a rikice-rikicen manoma da makiyaya tsakanin shekarar 2014 da 2015 kawai. A watan Fabrairu na shekarar 2016 kawai sama da mutane 300 aka kashe a lokacin da makiyaya suka kai hari wani qauye a yankin Agatu na jihar Benue. A wata maqala da jaridar Daily Nigerian a ranar 9 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, an ruwaito cewa “adadin Fulanin da aka kashe kuma ba makiyaya ba a Mambilla kawai sun kai sama da 800”. Wannan bai kunshi kasha-kashen da ke yawan faruwa a yankunan Zamfara da Sakkwato da Katsina ba.

A yadda al’amura ke tafiya a Nijeriya yanzu, da kuma yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta rasa niyya da kuzari karara wajen shawo kan al’amura, za mu iya cewa  muna kan hanyar tabarbarewa (Allah shi kyauta!). Idan ba mu sa lura ta tsanaki ba cikin lokaci, lallai za mu ci amanar magabatanmu, ta hanyar rusa rayuwar ‘ya’yanmu da za mu haifa nan gaba. Mun yarda cewa rikicin manoma da makiyaya ya gabaci mulkin Muhammadu Buhari. Duk da haka, rashin kulawarsa da rashin manufarsa da rashin fahimtarsa sun bayyana gazawarsa wajen ko da jajantawa a kan mutuwar dubban mutane ballantana ma ya ziyarci iyalan mamatan ya masu ta’aziyya, sun taimaka wajen bayyana da fadada bambance-bambancenmu wanda shi ke yamutsa damar samun dawwamammen zaman lafiya. A yau, kamar yadda wani mai sharhi ya ce, “Babu wani da ya tsira babu wani wuri da ake tsira. Kowa bai tsira ba kuma babu inda ake tsira. Ba mu gode wa raggon salon Buhari wajen magance matsaloli da sasanta rikice-rikice ba.” Kowane bangare na Nijeriya ya kama da wuta; daga tsaunin Mambila Plateau zuwa yankin Benue; daga yankin Kala-Balge zuwa shiyyar Ghandi a jihar Sakkwato. A yau, tafiye-tafiye da ake yi domin yawon shaqatawa  ta zama abar tsoro ga matafiya da iyalansu. Idan ‘yan fashi ba su kashe ka ba, za’a iya sace ka a yi garkuwa da kai. Abin da ke bakanta rai a duk wadannan al’amura da suke faruwa a yayin da rayukan ‘yan Nijeriya suka zama masu arha, shi ne rashin wata alama da gwamnatin APC ta nuna na magance wadannan matsaloli. Kenan basu dauki ‘yan Nijeriya da muhimmanci ba?

Me gwamnati ke yi yayin da karya doka ya zama jiki a cikin al’umma? Yayin da ba wanda zai yi tafiya ba tare da fargabar a sace shi a yi garkuwa da shi ba; Yayin da babu wanda zai fito daga gidansa ya wataya a yankinsu daga 9:00 na dare ba tare da fargabar tsageru za su yi masa fashi ba? Ya kasance kamar yadda aka rubuta a wani wuri cewa, “yanzu ne mafi lalacewar lokacin da za ka kasance dan Nijeriya ko a Nijeriya”. Abubuwa duk sun lalace! Mun yarda cewa gwamnati na yin ‘wani abu’ a kan lamarin, amma akwai abubuwa da yawa da ya dace a yi fiye da yin ‘wani abu’ a gaya wa duniya (musamman lokacin da ake asarar rayuka kullum). Mu ajiye siyasa a gefe. Ya kamata a saurari al’ummomin da abin ya shafa kuma a saurari korafe-korafensu. A yi kokarin gano da hukunta masu assasa matsalar, da kuma hukunta duk wani da yake da hannu wajen duk wata bahallatsa da take haifar da rikice-rikice. Babu wani shafaffe da mai!

Idan har ba a yanke hukuncin da ya dace ba kuma aka cigaba da sa son zuciya, to tabbas matsalolin Nijeriya a yanzu basu wuce wasan yara ba in an kwatanta da abin da zai faru gaba. An dai ce don gobe ake wankan dare kuma wanda ya tsufa yana bara bai yi bara yana yaro ba. Don haka, duk wanda ya ce ma gobe za ta yi kyau, tambaye shi: da wace jiyan?  

Ahmed Ibrahim ya rubata daga Abuja.

The post Rashin Tsari a Nijeriya: Bukatar Canji a 2019 appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here