Tsabar Rashin Tsaron Kasar nan ne ya Kawo Harin ‘Yan Bindiga a NDA – ‘Yan Najeriya

 

‘Yan Najeriya sun bayyana mamakinsu karara a kan yadda ‘yan bindiga suka afka har cikin NDA.

An samu rahotanni akan yadda ‘yan bindiga suka fada har barikin Afaka ta NDA da safiyar Talata.

Mutane da dama suna ganin tsabar rashin tsaron kasar nan ne ya janyo hakan, babu wanda zai tsira kenan.

Kaduna – ‘Yan Najeriya sun bayyana mamakinsu a kan yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki har NDA.

Daily Trust ta rawaito yadda ‘yan bindiga suka afka har barikin Afaka dake NDA da safiyar talata.

A nan ne suka harbe wani Lieutenant Commander Wulah da wani Lieutenant CM Okoronwo take a nan suka ce ga garinku.Sannan sun yi garkuwa da wani soja.

Wasu mutane suna ganin farmakin yana nuna irin tsabar rashin tsaron dake kasar nan ne, yayin da wasu suke ganin tabbas babu wanda ya tsira a kasar nan, Daily Trust ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here