Kungiyar Kwadago ta Kasa Reshen Jahar Kaduna ta Alakanta Rashin Tsaro a Jahar da Korar Ma’aikata da Gwamnatin Jahar ta yi

 

Kungiyar kwadago ta alakanta karuwar rashin tsaro a jahar Kaduna ta korar ma’aikata a jahar.

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin bikin ranar ma’aikata yau a babban birnin tarayya Abuja.

Kungiyar ta ce bata goyon bayan gwamnatin Kaduna akan matakin korar karin ma’aikata 5,000.

Kungiyar kwadago ta kasa reshen jahar Kaduna ta alakanta rashin tsaro a jahar da korar ma’aikata da gwamnatin jahar ta yi, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta ce gwamnatin Nasiru El-Rufai ta kori ma’aikata 30,000 tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2015.

Babban sakataren kungiyar hadaka ta AUPCTRE, Comrade Sikiru Waheed, shi ne ya bayyana haka yayin bikin ranar ma’aikata a Abuja.

AUPCTRE, reshen kungiyar kwadago ta kasa, ta ce za ta goyi bayan kungiyar kwadago kan makomar ma’aikatan a Kaduna.

Kungiyar kwadago tayi barazanar dakatar da al’amura a jahar Kaduna biyo bayan yunkurin gwamnati na korar ma’aikata 5,000.

Ya ce, “AUPCTRE na amfani da ranar ma’aikata ta 2021 don tabbatarwa ma’aikata da shugabannin su, karkashin jagorancin Comrade Ayuba Wabba cewa suna tare da kungiyoyin ma’aikata bisa nuna rashin goyon baya kan matakin da gwamna El – Rufai na korar karin ma’aikata 5,000 a watan da ya wuce, wanda hakan ya kai kusan korar ma’aikata 30,000 daga 2015 zuwa yau.

“Wannan na daga cikin dalilan karuwar rashin tsaro a Jahar Kaduna da makwabtan jahohi kamar Niger, Abuja da Kogi.” Kungiyar ta yabawa ma’aikata da jajircewar su duk da kalubalen da annobar COVID – 19 ta haddasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here