Yaƙar Zazzaɓin Cizon Sauro: Za’a Fara yi wa Yara Rigakafin Cutar

 

Za a fara yi wa yara rigakafin zazzaɓin cizon sauro na malariya a faɗin Afirka da zummar yaƙar cutar a duniya.

Zazzaɓin maleriya na daga cikin cutuka mafi girma da ke kashe ɗan Adam a wannan ƙarni, akasarinsu yara ƙanana da jarirai.

Samun rigakafi bayan kusan shekara 100, zai zama nasara mai girman gaske a harkar samar da magunguna a duniya.

Gwaji ya nuna rigakafin mai suna RTS,S yana aiki tun shekara shida da suka wuce.

Bayan ganin nasarar da aka samu a aikin gwaji a ƙasar Ghana da Kenya da Malawi, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ya kamata a fara amfani da ita a sauran sassan Afirka waɗanda suka fi haɗarin kamuwa da cutar.

Shugaban hukumar, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce wannan “abin tarihi ne”.

“Rigakafin maleriya ta yara da aka daɗe ana jira babbar nasara ce ga ilimin kimiyya da lafiyar yara da kuma kariya daga zazzaɓin maleriya”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here