Ta6ar6arewar tsaro a Arewacin Najeriya ya samo asali ne ta hanyar dakile hakkokin ‘Kananan Hukumomi da Gwamnonin Arewar suka yi, da kuma maganar ‘kaddara da Talakawa suka fiye yi idan alkaba’i ya same su. Wannan dalilin ne ya sa Gwamnonin mu suka dauki abin al’ada; su ‘ka’kaba ma Talakawa talauci, su sace musu dukiya, su hana su tsaro sannan ssu fito gidajen Rediyo suna cewa sun biya albashi akan kari.
Wannan al’amari ba karamin takaici yake bani ba. Gwamnonin mu suna da masaniya akan dukkan wannan masifar ta garkuwa da mutane da kuma kashe su kamar kiyashi da ake yi a kullu yaumin. Haka zalika, Gwamnonin mu da gangan suka hana ‘kananan Hukumomi hakkokin su da kuma ‘karfin da Kwansitushin ya ba su, dalili kuwa gashi nan muna gani. Yau an kashe mutum 40, gobe an sace mutum 30. In ba a nan ba, ina aka ta6a yin wannan dabbancin?
Read Also:
Suma kuma Elites din na Arewa, toshiyar baki ce ya sa suka yi gum da bakin su, da kuma kwadayin abin duniyar da bazai kaisu Qarni na 22nd ba daga su har iyalin na su da suka ba kariya a ‘Kasashen ‘ketare. Da ace suna yin tambayoyi wa Gwamnonin mu, akan ta6ar6arewar tsaro da rashin ko-in-kula, wallahi da yanzu abubuwan nan sun zama tarihi. FG ba ita kadai ce hakkin ya rataya a kan ta ba, hakki ne na SGs da kuma LGs da su yi kuwwa a kawo musu agaji. Sun yi kuwwar?
Allah ya tsinewa Gwamnan da ya bari ana kashe Talakwan sa, shi kuma ya kwashe masu tsaron ya kaisu Government House. Duk Gwamnan da ya ki yadda da tsarin LGs, Allah ka san hanyar da zaka fitar da shi daga kan wannan bakin mulkin dda suke mana, ka kawo musu jin kan mu, wadanda suke da kai na mutane ba wadannan gungun Dabba-Mutum din ba.
The post Rike kudaden Kananan hukumomi ya jawo matsalar tsaro a Arewa – Ahmad Ganga appeared first on Daily Nigerian Hausa.