Rikici Tsakanin APC da NNPP: Rundunar ‘Yan Sanda ta Soke Gangamin Kamfen a Kano
Rikici ya kaure tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da na New Nigeria Peoples Congress, NNPP.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta soke duk wani gangamin kamfen a jihar sakamakon barkewar rikici.
Rundunar yan sandan ta bayyana cewa an gargadi manyan jam’iyyun siyasa a Kano game da yiwuwar barkewar rikici a yau Alhamis.
Kano- Rundunar yan sandan jihar Kano ta soke duk wani gangamin yakin neman zabe a jihar saboda rikici da ya kaure tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Rikici ya barke kasancewar jam’iyyun biyu karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje na APC da Rabiu Kwankwaso na NNPP suka shirya gangamin karshe na zaben shugaban kasa a rana guda, rahoton Daily Trust.
An dai gudanar gangamin kamfen din na shugaban kasa da yan majalisun tarayya a ayu Alhamis, 23 ga watan Fabrairu ana saura kwana biyu zabe.
Yadda al’amarin ya faru Rigima ya fara ne bayan hukumomin yan sanda sun gayyaci shugabannin kungiyoyi uku na PDP, APC da NNPP zuwa wani taron gaggawa, suna masu gargadinsu kan yiwuwar rikici yayin kamfen din.
An tattaro cewa APC da NNPP sun yi watsi da shawarar jami’an tsaron sannan suka ci gaba da gangaminsu kamar yadda aka tsara wanda ya kai ga arangama tsakanin jam’iyyun.
Read Also:
Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu yan daba da ba a san ko su waye ba sun farmaki magoya bayan NNPP inda suka cinnawa motocinsu wuta a hanyar Zaria road.
Majiyoyi sun bayyana cewa suna a hanyarsu ta zuwa Kwanar Dangora don tarban Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP ne lokacin da lamarin ya afku.
A halin da ake ciki, wasu shugabannin jam’iyya mai mulki sun ce APC ta yi nufin fara gangaminta a Club road.
A gefe guda, NNPP sun yi nufin fara nasu a Kwanar Dangora kafin su garzaya gidan Kwankwaso a Miller Road wanda ke hanyar Club road. Sai dai kuma, yan daban dauke da muggan makamai na ta zarya a birnin tun a ranar Litinin, inda suka bar mutane da dama a baya, inji wata majiya.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da soke gangamin kamfen din
Da yake tabbatar da soke dukkanin gangamin kamfen din siyasa a jihar, DCP Muhammed ya ce:
“Ku tuna cewa manyan jam’iyyun siyasa uku APC, NNPP da PDP sun sanar da fara gangamin kamfen dinsu da aka shirya yi a ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairun 2023, a cikin birnin Kano.
“Biza la’akari da yanayin tsaro a jihar da kasar baki daya, kwamishinan yan sanda ya sammaci wakilan jam’iyyun siyasar uku zuwa taron gaggawa don neman mafita ga lamarin.
“Don haka aka ba da shawarar cewa dukkanin jam’iyyun su dage gangamin kamfen dinsu na shugaban kasa da majalisar dokoki zuwa wata rana bayan zaben 25 ga watan Fabrairu.”