Rikici ya Sake Kunno Kai Tsakanin ‘Ya’Yan Jam’iyyar APC a Zamfara

Sabon rikici ya sake kunno kai tsakanin ‘yayan jam’iyyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar Zamfara.

Jahar Zamfara na cikin jahohin da rikici ya hana jam’iyyar APC gudanar da taron gangaminsu har yanzu .

Manyan jigogin jam’iyyar har yanzu sun gaza jituwa da juna kan yadda za’a gudanar da shugabancin jam’iyyar a jahar.

Zamfara – Sabon baraka ya auku tsakanin yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jahar Zamfara kan zaben sabbin shugabannin jam’iyya a jahar.

Legit ta samu rahoton cewa barakan ya auku ne tsakanin yan bangaren tsohon gwamnan jahar, Abdul’aziz Yari da na Sanata Kabiru Marafa.

Zaku tuna cewa a watan Febrairun shekarar nan, an hada kai tsakanin bangaren Kabiru Marafa da na AbdulAziz Yari bayan shekaru uku ana rikici.

Amma bayan komawar Gwamnan jahar, Bello Matawalle, jam’iyyar APC a Yunin shekarar nan, an sake samun sabon rabuwar kai.

Wannan rashin jituwa ya wajabtawa uwar jam’iyyar jinkirta taron gangami da zaben shugabannin jam’iyyar a jahar.

Amma a ranar Laraba, jam’iyyar ta aikewa Shugaban hukumar INEC wasikar cewa ta zabi yau matsayin ranar gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a yau.

Sakamakon haka aka shirya zama tsakanin yan bangaren Yari da Marafa ranar Juma’a domin tattauna lamarin.

Me ya faru a zama?

Legit ta tattaro cewa a zaman, wani sashe yace lallai zasu cigaba da karar da suka kai kotu kan korar tsaffin shugabannin da akayi, yayinda daya sashen yace a gudanar da sabon zabe.

Daya daga cikin majiyoyin yace yan bangaren tsohon Shugaban jam’iyyar da aka rusa karkashin Yari, Lawal M Liman, sun lashi takobin komawa kotu kan korarsu da aka yi.

Daya daga cikinsu yace:

“Ba zamuyi musharaka a zaben ba saboda lamarin na kotu. Ba za’a yi da mu ba, kawai kotu zamu koma sai mun ga abinda ya turewa buzu nadi. Babu gudu babu ja da baya.”

Amma wani dan dayan bangaren yace:

“zamu yi zaben mu yau kuma mun gayyaci mabiyanmu daga gundumomi 147 dake jahar. Shugaban yan bangaren Marafa, Sirajo Maikatako ne jagoranmu.”

Ya kara da cewa har wasu manyan daga cikin yan bangaren AbdulAziz irinsu Mukhtar Shehu Idris (Koguna), Senator Lawali Shuaibu, Senator Tijjani Kaura, Abdulmaliki Zubairu, Abubakar Dantabawa na goyon bayan su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here