‘Yan Bindiga: Rikici ya Tsinke Tsakaninsu

 

Kaikayi ya koma kan mashekiya a dajin kauen Illela da ke yankin karamar hukumar Safana a jahar Katsina.

‘Yan bindiga kimanin dari uku, a karkashin kungiyoyi uku, sun gwabza kazamin rikici a tsakaninsu.

Rahotannin sun bayyana cewa fiye da mutum dari daga cikin ‘yan bindigar sun rasa rayukansu yayin rikicin a ranar Alhamis.

Wasu kungiyoyin ‘yan bindiga guda biyu da ke adawa da juna sun gwabza kazamin rikici a yankin kauyen Illela da ke yankin karamar hukumar Safana a jahar Katsina, kamar yadda rahoton HumAngle, wanda ya samo asali daga Daily Trust, ya nuna.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa an fafata rikicin ne a tsakanin yaran Mani Sarki da yaran Dankarami wadanda suka samu goyon bayan Abu Rada.Dukkaninsu shugabannin kungiyoyin ta’addanci ne da suka addabi Safana da kewaye.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa Daily Trust cewa an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama daga cikin ‘yan ta’addar suka samu raunuka.

Shaidun sun bayyana cewa tawagar ‘yan ta’adda ta kai wa Mani Sarki hari duk da ya yi hijira daga yankinsa zuwa dajin Illela bayan ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jahar Katsina.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here