Dambe ya Barke Tsakanin ‘Yan Majalisa

 

Wasu ‘yan majalisa sun bai wa hammata iska yayin wani zama na majalisar tarayya.

Wadanda suka kwashi damben ‘yan majalisar ne na yankunan da ake samun man fetur.

Take a wurin aka ga wasu daga cikin ‘yan majalisun suna tserewa don neman tsira.

Dambe ya barke yayin da wasu ‘yan majalisa na bangaren da ake samun mai suka je gabatar da wata muhimmiyar bukatarsu ga majalisa.

Vanguard bata riga ta tabbatar da sunayen ‘yan majalisar ba, amma tabbas masu wakiltar bangarorin da ake samun man fetur ne.

Fadan ya barke ne da misalin karfe 12:10pm yayin da shugaban kwamitin rikon kwarya na PIB, Hon. Mohammed Monguno ya gayyaci ‘yan majalisar don su gabatar da bukatunsu.

Har yanzu ‘yan majalisar suna ta ranta a na kare don gudun jikinsu yayi tsami sakamakon mugun damben da ake yi.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here