Rikicin Dakarun Kwastam da ‘Yan sumoga: An kashe mutane 2
Jami’an hukumar kwastam a Najeriya sun yi arangama da wasu da ake zargin ‘yan sumoga ne a yankin Abeokuta babban birnin Jahar Ogun.
Lamarin ya yi sanadiyyar kashe mutum biyu, yayin da ka raunata jami’an hukumar biyu, kamar yadda Premium Times ta rawaito kakakin hukumar na cewa.
Read Also:
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kwastam ɗin ne suka bi sawun wasu da suka zarga ‘yan sumoga ne bayan sun shigo da shinkafa kuma suka kama su a Kobape.
Sai dai wasu mutane ɗauke da makamai sun hana jami’an hukumar tafiya da su, inda nan take aka fara harbe-harbe.
Kakakin ‘yan sanda a jahar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa sun tura jami’ansu wurin.