Rili ya Taya Al’umma Musulmi Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

 

Hon. Muhammad Rili Ikara, na yi wa ɗaukacin al’ummar Musulmin duniya musamman ‘yan Jihar Kaduna da Ƙaramar hukumar Ikara murnar zagayowar Sabuwar Shekarar Musulunci a yau Laraba 1 ga watan Muharram 1445, wacce tayi daidai da 19 ga watan Yuli 2023.

Saƙon na zuwa ne ta hannun mataimakinsa na musamman a fannin watsa labarai Malam Yusuf Abubakar. Muhammad Rili, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda Allah ya kawo mu wannan sabuwar shekara cikin ƙoshin lafiya da kuma samun sabuwar gwamnati da ta kama aiki ‘yan watanni biyu baya.

Rili, ya yi fatan Allah (SWTA) da ya taimaki wannan sabuwar gwamnati tun daga matakin Tarayya zuwa Jiha, yay fatan Allah ya kame hannunwansu bisa aikata daidai, da kuma hana su aikata kuskure. Haka kuma yayi addu’ar Allah ya kawo dauwamemmen zaman lafiya da yalwar arziki a Ƙasar mu Nijeriya.

A yayin da yake bayani game da halin da ƙasar ta tsinci kanta a ciki na matsin tattalin arziki, Honarabul Rli, ya bai wa al’umma haƙuri bisa halin matsin da janye tallafin man fetur ya haifar ba hauhawar farashin kayan masarufi fa tsadar sufuri, yace, da yardar Allah wannan al’amari ya kusa kawo wa ƙarshe, kuma Gwamnatin Tarayya da ta jiha ƙarƙashin shugabancin Alhaji Ahmad Bola Tinubu da Sanata Malam Uba sani zasu kawo ƙarshen wannan tarnaƙi nan ba da daɗewa ba.

Haka kuma, ya buƙaci a sanya Gwamnati da Shugabanni a dukkan matakai cikin addu’o’in fatan samun inganyacciyar nasarar da zata sanya farin ciki a cikin zukatan ‘yan Nijeriya.

Allah ya taimaki Nijeriya, a ƙarƙashin jagorancin Asiwaju Ahmad Bola Tunubu.
Allah ya taimaki Jihar Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Malam Uba Sani.

SA HANNU:
Abubakar Yusuf
(Adviser on Media)
19/07/2023

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here