2023: Da Gaske ne Gwamnan Jahar Rivers Yana Neman  Kujerar Shugaban Kasa ?

 

Gwamna Nyesome na jahar Rivers Wike ya ragargarji masu adawa da gwamnatinsa a jaharsa.

Gwamnan ya ce wasu daga cikin yan adawa ne suka yada fastocin yakin neman zaben shugabancin kasarsa a wasu jahohi.

Gwamnan, ya shaida cewa, baya sha’awar tsayawa takara a babban zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Dangane da jita-jitar da ake yadawa game da takarar shugabancin kasarsa a 2023, gwamnan Jahar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana cewa ba shi da sha’awar tsayawa takara a babban zabe mai zuwa.

PM News ta ruwaito a wata tattaunawa da aka yi a gidan talabijin na Channels a Port Harcourt, Wike ya ce yan adawar sa ne suka shirya yadda fostocin yakin neman zaben sa suka dinga yawo a Abuja satin da ya gabata, wanda ya janyo zargin cewa yana neman kujerar lamba daya a kasa.

Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnan ya ce duk da yana da yancin neman takarar, abin da ke gaban shi yanzu shi ne kawo ci gaban dimokradiyya ga al’ummar Rivers.

Ya ce: “Daga Disambar shekarar da ta gabata zuwa yanzu, muna ta kaddamar da ayyuka. To mutane na ganin cewa da irin ayyukan da muke yi, ina da niyyar tsayawa takarar shugabancin kasa ne.”

Wike ya kuma ce bayan kwaskwarimar da majalisa ta yi wa dokar zabe, ba zai yi daidai ba a yi zabe ta ba tare da amfani da card reader wurin tabbatar da ingancin kuri’un da aka kada.

Ya ce mafi yawancin yan majalisar suna mayar da hankulansu ne kan batun yadda za su zarce a zabe don haka sukan yi gyarar dokar zaben ne a lokacin da zai amfane su da jam’iyyunsu.

Gwamnan ya kara da cewa: “Mene yasa shugaban kasa ya ki saka hannu kan dokar yiwa dokokin zaben garambawul, saboda mene? Saboda APC ta fada wa shugaban kasa cewa idan ya saka hannu a kan dokar, zai iya fadi zabe. Don haka, kada ka saka hannu. Don haka shugaban kasar bai saka hannu ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here