Rokan da Kasar Sin ta Harba Sararin Samaniya a Watan Afrilu 2021 na Shirin Dawowa Duniya

 

Wani Rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya na shirin fadowa duniya wannan makon.

Masana sun bayyana cewa ba’a san takamammen inda wannan roka zai fadi ba.

An lissafa Abuja cikin jerin biranen da roka ka iya fadowa.

Wani rahoton NBC News ya nuna cewa rokan da kasar Sin ta harba sararin samaniya a Afrilun 2021 na shirin dawowa duniya yau Asabar, 8 ga Mayu, ko Lahadi 9 ga Mayu, bisa hasashen masana.

A cewar Rahoton, rokan mai girman gida mai tsauni 10 na yawo a sararin samaniya yanzu hakan da gudun mil 18,000/hr.

Yayinda ba bakon abu bane sassan roka ya fado duniya, wannan ya zama abin damuwa saboda rokan ya bace ne kuma babu tabbacin inda zai fadi.

Masana Kimiya sun bayyana cewa yiwuwar idan ta fado za ta kashe mutum na da kamar wuya, amma zai yiwu.

An bayyana jerin biranen da ake ganin da yiwuwar ta fado. Biranen sune; New York, Los Angeles, Madrid, Rio de Janeiro, Beijing, da birnin tarayyar Abuja.

Masanan sun kara da cewa an fi kyautata zaton rokan zai fadi ne cikin teku.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here