Ina Rokon Jinkai da Gafara, Ba Zan Sake Aikata Irin Wannan Laifin ba – Kasungurmin ‘Dan Bindiga

 

Kasungurmin dan bindigan da aka kama ya fallasa sunayen wasu da yake aiki dasu a daji.

Ya kuma roki jama’a su yafe masa, inda ya ce shi dai ya rantse ba zai sake irin wannan aikin ba.

Ya kuma bayyana irin kudaden da ya karba na fansa daga wasu mutanen da ya yi garkuwa dasu.

Kaduna – Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jahar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta rawaito.

Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta’annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.

A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami’an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.

“Ina rokon jinkai da gafara; Ba zan sake aikata irin wannan laifin ba.”

Dangane da wasu ayyukan da ya yi, ya ce:

“Mutum na farko da muka yi garkuwa da shi shine Abdul; sun biya kudin fansa N200,000; akan Alhaji Umaru, mun karbi N500,000, Wani kuma Alhaji Birau; sun biya jimillar naira miliyan uku sannan dayan kuma shine Alhaji Ibrahim wanda ya biya N700,000. ”

Samaila ya kuma bayyana sunayen wasu daga cikin ‘yan kungiyar. “A cikin Rigachikun, akwai Yusuf, Sale, Gomi, Nasiru, Tukur, Banki, Magaji.

“Sannan a yankin Kirama, akwai Musa, Kadi, Oria, Ibrahim, Bala, Rebo, Gaia, Malan, Osama, Babangida, Abubakar da Sule. Ba zan iya tuna sunan wanda ya bar mu ya koma wurin Babangida, Suleiman da Sule.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here