Matsalolin Yankin: Gwamnoni da Sarakunan Arewa Sun Shiga Ganawa a Jahar Kaduna

 

Gwamnoni da Sarakunan Arewa sun shiga ganawa a Kaduna don tattauna lamarin Arewa.

Taron ya samu halartan kusan dukkan masu fada a ji a Arewa.

Daga cikin lamuran da za’a tattauna kan lamarin kudin harajin VAT.

Kaduna – Shugabannin yankin Arewacin Najeriya sun taru a jahar Kaduna domin tattauna matsalolin tsaron, zaman lafiya da cigaba da suka addabi yankin.

Wadannan shugabanni sun hada da gwamnonin jahohin Arewa 19 karkashin jagorancin gwamnan Plateau, Simon Lalong; da Shugaban Sarakunan gargajiyan Arewa, Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa’ad.

Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya karbi bakuncinsu ne ranar Litnin, 27 ga watan Satumba, 2021, a farfajiyar taron gidan gwamnatin Kashim Ibrahim.

Wannan ya biyo bayan ganawar farko da Shugabannin sukayi a watan Febrairu, 2021.

Su wa ke hallare yanzu haka a jahar Kaduna?

Daga cikin wadanda ke hallare cikin gwamnoni akwai gwamnan Plateau, Simon Lalong; Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, gwamnan Katsina, AMinu Masari; da gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu.

Hakazalika akwai gwamnan jahar Borno, Babagana Zulum; Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa; gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru; gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, dss.

Sarakunan Arewa kuma akwai Mai alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad; Shehun Borno, Etsu Nupe, dss.

Wa ke jagoran zaman?

Gwamnan Plateau wanda ke jagorantar zaman ya bayyana abubuwan da zasu tattauna kai wannan karon.

A jawabin da ya saki a shafin sakataren yada labaransa a Facebook, Lalong yace sun taru ne domin samun rahotanni daga kwamitocin da suka nada Febrairu don duba matsalar tsaron da yankin ke fama da ita.

Yace:

“Zamu duba irin abubuwan da muka samu yi wajen dakile tsagerun yan bindiga, garkuwa da mutane, ta’addanci da kuma sanin abinda zamu yi nan gaba.”

“Hakazalika, zamuyi dubi kan wasu lamurorin da suka taso a fadin tarayya makonnin baya domin fitar da matsayinmu. Daga cikinsu akwai lamarin kudin harajin VAT.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here