Rikicin Sudan: Dakarun RSF Sun Zargi Sojojin ƙasar da Far wa Sansanoninsu

 

 

Dakarun RSF da ke faɗa a Sudan, sun zargi sojojin ƙasar da far wa sansanoninsu da ke yankin Kafuri da birnin Bahri da kuma arewacin Khartoum.

Dakarun sun ce sojojin sun kai hare-hare ta sama da kuma amfani da makaman atilari.

Zargin na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Sudan suka amince da bukatar shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu na tattaunawar gaba-da-gaba, sai dai RSF ba su kai ga amsa bukatar ba.

Dakarun RSF sun wallafa a shafin Facebook a safiyar yau Alhamis cewa “Dakaru masu tsassaurar ra’ayi na far wa sansanonin mu da ke yankin Kafuri ta hanyar amfani da hare-hare ta sama da kuma makaman atilari. Dakarun mu sun fafata da sojojin.”

Sai dai sojojin Sudan ba su ce uffan ba kan wannan zargi kuma ba za mu iya tabbatar da ikirarin na RSF ba kaow yanzu.

Sudan ta Kudu dai na jagorantar shiga tsakani na ganin an ƙara tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta kawo karshe a daren yau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here