Dalilin da Yasa Sojojin Najeriya Suka Rufe Babbar Gadar Niger
Wasu sojojin Najeriya sun rufe babbar gadar Niger wacce ke tsakanin garin Onitsha da Asaba yayin da mazauna Anambra ke sauraron sakamakon zaben.
Har ila yau, an ji karar harbe-harben bindiga yayin da mazauna garin suka dinga gudun ceton rai a fadin garin duk da cunkoson da aka samu.
Wannan lamarin yasa mutanen yankin ballantana matafiya suka tsaya a wurin cunkoson tare da sauka daga ababen hawansu.
Anambra – An samu rikici tare da tashin-tashina a wuraren gadar Niger ta biyu da ke Onitsha bayan sojoji sun rufe dukkan bangarorin gadar tare da hana ababen hawa yawo.
Wakilin Legit.ng da ke kan hanyarsa ta zuwa Asaba tare da wasu fasinjoji ya sauko daga abun hawansa tare da yin tattaki zuwa dayan bangaren gadar domin cigaba da tafiye-tafiyen.
Read Also:
A yayin wannan al’amarin ne, sojoji suka dinga harbi a iska domin tsarotar da matafiya wadanda suka harzuka da cunkoson kan titin.
An rufe titin ne bayan samu umarni daga sama Wani matafiyi wanda ya bayyana sunansa da Obinna ya sanar da Legit.ng cewa sojoji sun yi ikirarin cewa sun rufe gadar ne sakamakon umarin da suka samu daga sama.
A yayin magana da harshen Ibo, ya ce:
“Sun ce gwamnatin tarayya ce ta umarcesu da su rufe titin har sai an kammala sanar da sakamakon zabe.”
Obinna ya koka da cewa: “Ta yaya haka ya shafe mu? Wasu daga cikinmu za su wurare masu nisa ne kuma suke wahalar da mu kamar haka.”
A dayar hanyar da ke kaiwa gadar Onitsa zuwa Asaba, sojoji sun tsare jama’a inda suka saka masu wucewa suna daga hannayensu sama.
Masu babur din Achaba sun yi amfani da wannan damar wurin damawa. Sun dinga daukar fasinjojin da suka kagu da su gansu a inda ya dace, ballantana masu tafiya zuwa filin jirgi.
Daga farkon gadar zuwa karshen ta, ‘yan achaba sun dinga karbar naira dari biyar domin fasinja da kayansa.