Gyara: Gwamnatin Tarayya Zata Rufe Filin Jiragen Sama na Murtala Muhammed da ke Legas

 

Sabon ministan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sufurin jiragen sama da cigaban samaniya, Festus Keyamo, ya ce a rushe wurin ajiye jiragen sama na Dominion da EAN da ke MMIA 2 a Legas.

Ministan ya ce za a yi hakan ne domin shirin gyara da fadada filin tashin jiragen saman da ake shirin yi.

Keyamo ya bada umurnin yayin da ya ke duba filin jiragen saman a ranar Alhamis, irinsa na farko tunda ya kama aiki a matsayin minista.

Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama ya bada umurnin rushe wuraren ajiye jiragen sama na EAN da ke fiilin tashin jirage na Murtala Mohammed ta Biyu (MMIA 2), da ke Legas. Ya ce a rushe su nan take.

A cewar Daily Independent, ministan ya ce rushewan zai bada daman a fadada filin sauka da tashin jiragen saman.

Keyamo ya yi korafi kan rashin tsafta a MMIA yayin ziyararsa

Keyamo ya bada umurnin ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, a lokacin da ya ziyarci filin tashin jirage na Legas domin duba halin da ya ke ciki.

Ministan ya nuna bacin rai bisa yadda aka bar filin jirgin cikin kazanta.Ya bada umurnin a tsaftace wurin nan take.

Keyamo na daya daga cikin ministoci 45 da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta a Fadar Shugaban Kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugaba Tinubu ya mika sunayen mutane 48 da ya ke son nada wa minista domin majalisar dattawa ta tantance su.

Yadda Keyamo ya zama ministan Tinubu

Amma, majalisar ta tantance mutane 45 ne kawai cikin 48 din, inda ta bada dalilin batun tsaro na dage tantance sauran mutanen uku.

Keyamo, a baya ya yi aiki a matsayin karamin ministan kwadago a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Yayin da ya ke aiki a matsayin minista, Keyamo ya soki lakabin mukamin karamin minista, mukamin da ya ke rike da shi. Hakan ya janyo cece-kuce tsakanin masu bibiyan harkokin siyasa a Najeriya.

A yayin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ministan ya yi aiki a matsayin kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com