Batanci ga Annabi(S.A.W) : An Rufe Kwalejin Ilmin Shehu Shagari

Hukumomi a kwalejin ilmin Shehu Shagari sun umurci dukkan daliban makarantar su koma gida.

Jawabi ya nuna cewa an rufe kwalejin ilmin har ila ma sha’aLLahu sakamakon abinda ya faru da safe.

An kashe wata dalibar kwalejin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi.

Sokoto- Hukumar kwalejin ilmi ta Shehu Shagari dake jihar Sokoto, Arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da rufe makarantar bisa abinda ya auku da safiyar Alhamis.

Kwalejin, a jawabin da ta saki da rana ta bayyana cewa sakamakon abinda ya faru da safiyar Alhamis, an rufe makarantar kuma dalibai su koma gida.

A jawabin da Legit ta gani a Tuwita, an ce dukkan dalibai suyi gaggawan komawa gida.

A cewar jawabin:

“Sakamakon rikicin dalibai da safiyar nan a kwalejin, hukumomin kwalejin sun yanke shawarar rufe makarantar har sai baba ta gani.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here