Shin Rufe Layukan Waya na da Alaƙa da Zanga-Zanga ?

 

An wayi gari ranar Litinin mutane a Najeriya na tururuwa zuwa ofisoshin kamfanonin sadarwar wayar hannu domin isar da ƙorafi kan rufe masu layukan waya.

Hakan na zuwa ne bayan a cikin ƙarshen mako masu amfani da layukan waya sun tsinci kansu cikin ruɗani, bayan gaza yin kira ko amsa kira daga ƴan’uwa da abokan hulɗa na kasuwanci.

Bayanai na cewa miliyoyin mutane ne suka shiga cikin irin wannan hali a faɗin ƙasar ta Najeriya.

Kamar sauran ƙasashen duniya, mutane da dama a Najeriya sun dogara da wayoyin hannu wajen tafiyar da sana’o’i da sauran harkokin rayuwa.

Yayin da wasu ke amfani da kiran waya, wasu kuma na amfani da sadarwar intanet da suke samu daga kamfanonin wayar hannu wajen tafiyar da lamurran nasu.

Rufe layukan wayar ya jefa mutane cikin damuwa yayin da wasu suka fara yaɗa labaran da ke cewa rufe layukan na da alaƙa da zanga-zangar da ta mamaye duk wasu muhawarori da ke gudana a ƙasar.

Matasa ne ke shirya zanga-zanga, wadda suka ce za su fara a farkon watan Agusta.

BBC ta nemo gaskiyar bayani game da abin da ya haifar da rufe layukan wayar.

Dalilan rufe layukan waya

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta tabbatar wa BBC cewa tabbas an rufe layukan masu amfani da wayoyin salula a fadin ƙasar ta Najeriya.

Sai dai an rufe layukan ne sanadiyyar cikar wa’adin da hukumomi suka bayar na haɗa layukan wayar da lambar ɗan ƙasa ta NIN, wato ‘National Identification Number’.

A baya dai hukumomi a Najeriyar sun riƙa shata wa’adi suna ɗagawa na haɗa layukan wayar da lambar zama ɗan ƙasa.

Wani jami’in hukumar ya shaida wa BBC cewa “wa’adin da hukumomi suka shata na rufe layin wayar duk wanda bai hada layin wayarsa da lambar ɗan ƙasa ta NIN ba ne ya cika.”

Haka nan ma ƙungiyar kamfanonin waya na Najeriya (ALTON) sun fitar da wata sanarwa a ranar Litinin.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun shugabanta na ƙasa, Injiniya Gbenga Adebayo ta ce “ta kwashe watanni tana aikin tacewa da tantance bayanan layukan da aka yi wa rajista da kuma na shaidar zama ɗan ƙasa da take da shi a rumbunta na ajiye bayanai”.

“Masu amfani da layukan waya da aka rufe cikin kwanakin nan su ne waɗanda aka gano bambance-bambance ko abubuwa masu karo da juna a cikin bayanan da suka bayar na layin wayarsu da lambar zama ɗan ƙasa.”

Shin rufe layukan wayar na da alaƙa da zanga-zanga?

Mutane da dama sun riƙa yaɗa labarin cewa rufe layukan wayar na da alaƙa da zanga-zangar da matasa ke shiryawa a ƙasar ta tsadar rayuwa.

Sai dai a cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa (ALTON) ta ce lamarin ba haka yake ba.

Sanarwar ta ce “Ko kadan, babu alaƙa tsakanin abubuwan biyu. Wa’adin haɗa layin waya da lambar zama ɗan ƙasa ya cika ne ranar 31 ga watan July, 2024”.

Yadda za ku buɗe layukan wayarku

Ƙungiyar masu kamfanonin wayar ta kuma bayyana yadda mutanen da aka rufe wa yaukan za su iya buɗe su.

A cikin sanarwar, ta ce mutane na iya amfani da hanyar latsa wasu lambobi domin tantance matsayin layukansu da kuma buɗe su.

Sai dai sanarwar ta ce idan har aka kasa buɗe layi ta hanyar amfani da labobin mutane za su iya zuwa ofisoshin kamfanonin waya domin kai ƙorafi.

Bayanai daga Hukumar sadarwa ta Najeriya sun nuna cewa akwai masu amfani da wayar hannu miliyan 219,005,878 a ƙasar.

A watan Fabarairun 2020 ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar sadarwa ta ƙasar (NCC) da hukumar rajistar ƴan ƙasa ta NIMC su fara aikin haɗa duk wani layin waya da lambar zama ɗan ƙasa.

Gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa za a ɗauki matakin rufe duk wani layin waya da ba a haɗa shi da lambar zama ɗan ƙasa.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yunƙuri na shawo kan matsalolin tsaro.

Al’ummar ƙasar sun sha kokawa kan yadda masu aikata laifuka, musamman masu garkuwa da mutane ke amfani da layukan waya wajen karɓar kudi daga hannun ƴan’uwan waɗanda suka yi garkuwa da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here