Rufe Makarantu a Jahar Kaduna: Iyayen Yara Sun Fara Tura su Gurin Koyan Sana’o’i

 

Iyayen yara a Kaduna sun bayyana cewa suna tura yaransu zuwa koyon sana’o’i a yayin da makarantun jahar ke rufe.

Wani iyayen sun bayyana cewa yaransu na koyon sana’o’i kamar dinki da walda da wasu sana’o’in da za su amfane su.

Wasu iyayen yaran sun kuma ce suna koyar da yaransu karatu a gida tare da shawartar gwamnati ta rika koyar da yaran ta talabijin.

A yayin da Gwamna Nasir El-Rufai na Jahar Kaduna ya rufe makarantun jahar sakamakon sace-sacen dalibai da masu garkuwa ke yi, iyayen yara sun fara tura su wuraren koyon sana’o’i, rahoton Peoples Gazette.

A ranar 6 ga watan Agusta ne Gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta sanar da dage komawa makarantun har wani lokaci a nan gaba.

Gwamnati ta ce rufe makarantun ya fi zama alheri ga yaran makarantan a yayin da sace dalibai don karbar kudin fansa ke kara yawaita musamman a yankin arewa.

Ibrahim Yusuf, wani mutum mai ‘ya’ya biyu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Juma’a a Kaduna cewa tsare yaran ya fi muhimmanci don haka ya bukaci gwamnati ta rika amfani da rediyo, talabijin da soshiyal midiya don koyar da yara a gida.

Mr Yusuf ya bayyana cewa bai bar yaransa kara zube ba a gida.

A cewarsa, suna zuwa shagonsa tare da shi suna koyon walda kamar yadda Peoples Gazette ta ruwaito.

Wata mahaifiya, Hauwa Muhammad, ta ce ta tura danta mai shekara 10 zuwa wurin koyon dinki.

Ta yabawa gwamnatin jahar Kaduna bisa daukan matakin kare yaran tana mai kira ga gwamnatin ta inganta tsaro domin daliban su samu damar komawa makaranta.

Ina koyar da yara na karatu a gida, wani mahaifin dalibai

Kazalika, Abel ya bayyana cewa yana koyar da yaransa idan ya dawo daga aiki karfe 4 na yamma sannan yana basu karatun da za su yi idan baya nan don kada su yi zaman banza.

Ya bukaci iyaye kada su kyalle yaransu su rika yawon gararamba a gari amma su basu kariya sannan su rika koyarda su tare da koya musu ayyukan gidan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here