Mutuwar Sheƙau: Rundunar Sojojin ƙasar nan Tayi Magana Kan Rahoton
Rundunar sojojin ƙasar nan tayi magana kan rahoton dake nuna cewa shugaban Mayaƙan Boko Haram, Abubakar Sheƙau, ya sheƙa lahira.
Sojojin sun ce a halin yanzun ba zasu iya tabbatar da labarin ba amma suna cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Rahoton dai ya bayyana cewa Sheƙau ya rasa ransa ne yayin da abokan hamayyarsu ISWAP suka kai musu hari a dajin Sambisa.
Rundunar sojojin Najeriya tace ta fara binciken rahoton dake nuna cewa shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau, yaji mummunan rauni kuma ya mutu.
Read Also:
Wani rahoto ya bayyana cewa, Abubakar Shekau yaji mummunan rauni yayin da yayi ƙoƙarin kashe kansa don kada abokan hamayyarsa ISWAP su kama shi a wata fafatawa da suka yi.
Rahoton ya kuma bayyana cewa shugaban Boko Haram ɗin ya sheƙa lahira bayan jiwa kansa mummunan rauni, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Rahoton yace:
“Mayaƙan ISWAP sun mamaye shugaban Boko Haram tare da mutanen sa ranar Laraba a dajin Sambisa, inda suka buƙaci ya miƙa kansa.”
“A wannan lokaci ne Abubakar Sheƙau ya harbi kansa a ƙirji don kada yan ISWAP su kama shi, harbin yaji masa mummunan rauni.”
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar soji ta ƙasa, Muhammed Yerima, kan rahoton bai musanta ba kuma bai tabbatar ba.
“Muna kan bincike ne.” Muhammed Yerima ya bada amsar saƙon da aka tura masa kan rahoton.