Rusau: Gwamnatin Jahar Gombe ta Biya Wadanda Abin ya Shafa Makudan Kudade
Gwamanatin jahar Gombe ta bayyana biyan diyyar filaye da gidaje a jahar.
Gwamnatin ta bayyana rusa gidajen a matsayin aikin cigaban jahar.
Kimanin N873 ne gwamnatin ta rabawa wadanda abin ya shafa.
Gwamnatin jihar Gombe a ranar Laraba ta bayyana cewa an biya N873m a matsayin diyya ga masu filaye a jihar, Punch ta ruwaito.
Read Also:
Da yake bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron zartarwar jihar wanda Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta, kwamishinan yada labarai, Alhassan Ibrahim, ya ce asalin filin mallakar gwamnati ne, ya kara da cewa an biya kudin ne saboda dattakun gwamnan.
Ibrahim ya kara da cewa an yi hakan ne don amfanin jama’a, yana mai cewa hakan ya ta’allaka ne ga ci gaban jahar.
“Zuwa yanzu mun biya N873, 214,193,43; wannan shi ne jimillar diyyar da muka biya kan filaye daban-daban da muka samo don ayyukan ci gaba. Dukkanin diyyar an biya kuma ba a bin gwamnati bashi.
“An biya diyya don gine-gine a cikin jahar. Gwamna cikin girmamawa ya ce tunda filin mallakar gwamnati ne, bari mu biya su wani abu. Kasancewar aikin na ci gaba ne,” In ji shi.