Ruwan Sama Mai Tsanani Ya Kashe Mutane 5 Tare da Lalata Gonaki 1,567 a Jahar Bauchi

 

Wani ruwan sama mai tsanani ya lakume rayukan mutun 5 tare da lalata amfanin gonakin mutane a jahar Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan wanda aka shafe sama da awa 20 ana tafkawa ya haifar da ambaliya.

Shugaban ƙaramar hukumar Jama’are, Jarma, ya tabbatar da faruwar lamarin a yankin da yake jagoranci

Bauchi – Wani ruwan sama mai tsanani da ya haifar da ambaliya ya lalata gonakin mutane akalla 1,567 a karamar hukumar Jama’are, jahar Bauchi, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Mamakon ruwan wanda aka shafe sama da awanni 20 ana yi, ya lalata amfanin gonakin mutane a ƙauyuka 7 dake yankin.

Shugaban ƙaramar hukumar Jama’are, Sama’ila Jarma, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

A cewar Jarma, kauyukan da ambaliyar ruwan ya shafa sun haɗa da Jogiyal, Yola, Doko-Doko, Gongo, Kabigel, Digiza da Massalachin Idi duk a yankin karamar hukumar Jama’are.

Menene musabbabin ambaliyar?

Shugaban ya bayyana cewa tekun Jos ne ya yi ambaliya biyo bayan wani mamakon ruwa da aka tafka wanda ya shefe awanni ana yi ranar Talata.

Vanguard ta ruwaito a jawabinsa yace:

“Mun gano gawarwaki biyar a cikin ruwa a yankin da ambaliyar ta shafa. Ɗaya daga cikin gawar daga kauyukan da lamarin ya shafa ya fito yayin da har yanzun ba’a gano asalin sauran mutum 4 ba.”

“Mun rika mun binne gawarwakin bayan mun yi iyakar yin mu mugano inda mutanen suka fito. Amma mun ɗauki hotunansu ya Allah wasu zasu zo nema.”

Wane mataki gwamnati ta ɗauka? Jarma ya kara da cewa gwamnatinsa ta kaddamar da kwatin da zai binciko asarar da aka yi domin mika wa gwamnatin jaha ta ɗauki mataki.

A jawabinsa yace gwamnatinsa ta raba kayan abinci da sauran abubuwan rayuwa domin rage raɗaɗi kafin gwamnatin jaha ta shigo cikin lamarin.

An tafka ruwan da ba’a taba irinsa ba cikin shekara 100

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here