Bada Cek Din Bogi: Shugaban kasar Ruwanda ya Yafewa Tsohon Firaministan kasar, Pierre Damien Habumuremyi 
Shugban kasar Ruwanda Paul Kagame ya yafe wa tsohon firaiministan sa Pierre Damien Habumuremyi wanda aka yanke wa hukuncin shekara uku gidan yari saboda fitar da cek din bogi da ya yi.
An kulle tsohon firaministan shekarar da ta gabata sakamakon cek din bogi da ya yi amfani da shi wurin biyan masu binsa bashi a jami’ar sa mai suna Christain University of Ruwanda, wadda tuni aka rufe ta.
Yayin tuhumarsa, Habumuremyi ya ce ya bada cek din ne a matsayin garanti jami’ar za ta biya basukan da ake binta sannan kuma ya basu wani dan kudi tare da cek din.
Tare da hukuncin da aka yanke masa an sa shi ya biya miliyan 892 kudin Rwanda.
A cewar kafafen yada labarai na jahar, za’a dakatar da amfanin asusunsa na banki da kuma kwace masa kadarori har sai ya biya kudin.
Dan tsohon firaiministan Apollo Mucyo, wanda ya yi kamfen don sakin shi ya rubuta a shafin instagram yana cewa ”zuciyata a cike take, ina farin ciki da ba zan ma iya kwatantawa ba.
”Na godewa Allah son da nake yiwa kasa ta yana nan kamar yadda yake da… Nagode da karamcin nan.
Habumurmyi mai shekara 60, shi ne firaiministan kasar na tara, ya yi aiki daga shekarar 2011 zuwa 2014 wanda kafin nan ya yi ministan ilimi na wata biyar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here