Sababbin Matakan Yaki da Annobar Cutar Korona Karo na Biyu

Ƙwararru a harkar lafiya a Najeriya sun yaba da wasu sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar cutar korona ya sake ɗauka.

A ranar Litinin ne kwamitin shugaban ƙasar Najeriya da ke yaƙi da annobar cutar korona ya sake bayar da umarni kan bin wasu sabbin matakan yaƙi da cutar a yayin da take sake hauhawa a karo na biyu.

Wani masani kuma ƙwararre a harkar lafiya Dr Nasiru Sani Gwarzo ya ce matakan sun dace kuma lokacin saka su ya yi, “dama tun farkon kafa wannan kwamiti na faɗa cewa hakan ya dace don gwamnati na buƙatar ta dinga sa ido kan yanayin annobar.”

“Ta yadda duk lokacin da ta ga yanayin annobar ya sauya akala ko kuma ta zo da wani yanayi daban da ba a san shi ba to a nan ne wannan kwamiti yake da alhakin yin hangen nesa don kare yaɗuwar abin da zai je ya zo,” in ji Dr Gwarzo.

Me sabbin matakan suka ƙunsa?

Daga cikin umarnin akwai wanda aka bai wa ma’aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

A cewar kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, duka makarantu a faɗin ƙasar za su zama a rufe har zuwa watan Janairun 2021.

Kwamitin ya bayyana cewa gidajen rawa da wuraren shan barasa da kuma wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a ƙasar.

Sannan kuma kwamitin ya bayar da umarnin rufe gidajen abinci.

Haka kuma gwamnatin ta saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri ka da ya ɗauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake ɗauka a baya.

Gwamnatin ta ƙayyade tarukan addini su zama kasa da kashi 50 na inda wuraren ibada ke ɗauka, domin tabbatar da ba da tazara da kuma sanya takunkumi.

Boss Mustapa ya ce dukkan taron da za a yi ya wuce mutum 50 to a tabbatar da an yi shi a buɗaɗɗen waje maimakon a ɗakin taro.

Haka nan ababan hawa su ɗauki kashi 50 na fasinjan da suke iya ɗauka domin bin dokar bayar da tazara.

Ya ƙara da cewa an ɗauki bayanan matafiyan da suka shigo ƙasar daga waje su 163,818 kuma an wallafa a shafin gwamnatin.

Shin annobar ta fi zafi a wannan karon?

Ƙwararru sun yi amannar cewa annobar ta cutar korona ta fi yin ƙamari a wannan karon bisa la’akari da sabbin alƙaluman da ake samu na masu kamuwa da ita a kullum.

Dr Gwarzo ya ce gaskiya ne annobar ta fi tsanani ta kuma fi zafi. “Idan ka lura a da mace-mace da ake yi ana fargabar cewa cutar korona ce amma ana tababa, sai da aka yi gwaje-gwaje aka tabbatar.

“Amma a yanzu jama’a da kansu duk wanda ka tambaya za ka samu a ƙalla ya san wani da cutar korona ta kashe. Dalili kuwa shi ne yawanta ya ƙaru.”

Ƙwararren ya ci gaba da cewa akwai abin tsoro ganin cewar yadda take saurin kisa ma ya ƙaru.

“Akwai waɗanda ba ta yi musu da daɗi, ganin cewa kuna tare da mutum kwana ɗaya biyu idan ya kamu kafin ka ce me ye sai yanayin jikinsa ya jirkice ya shiga wani hali. Nan da nan sai ka ji an ce wane ya mutu,” a cewar masanin.

Shin sabon nau’in cutar korona ya shigo Najeriya?

A baya-bayan nan ne Birtaniya ta sanar da gano wani sabon nau’in cutar ta korona wanda ya fi saurin yaɗuwa, har ma hakan ta sa wasu ƙasashe da dama suka hana jiragen Birtaniyan shiga ƙasashensu.

A yanzu haka kuma ƙasar Afirka Ta Kudu ma ta sanar da ɓullar sabon nau’in cutar a can. Hakan ya fara jefa fargaba a zuƙatan wasu yan Najeriya.

Sai dai duk da cewa har yanzu babu tabbaci a hukumance kan ɓullar sabon nau’in a Najeriya, Dr Gwarzo ya ce ba abin mamaki ba ne idan ma ya shiga ɗin.

“A dokar likitanci ta yaɗuwar annoba duk inda take a duniya to za ta iya yaɗuwa zuwa sauran sassan duniyar.

“Za a shiga jirgi mutum yana Birtaniya da safe amma zuwa yamma yana Najeriya. Wannan yanayi ya kan haɓaka yaɗuwar cututtuka.

“Babu mamaki wannan sabon nau’i tuni ya fantsama a duniya ya zo Afirka, wataƙila ma ya shigo Najeriya duk da cewa dai babu tabbaci amma mu a likitance ba abin mamaki ba ne idan hakan ta faru,” in ji Dr Gwarzo.

Me ya kamata mutane su yi a yanzu?

A yanzu dai babban abin da ke zuƙatan mutane shi ne me ya kamata su yi a daidai wannan gaɓa.

Ƙwararren ya ce babban abin da ya kamata mutane su yi a yanzu shi ne su yi karatun ta nutsu, su ci gaba da bin matakan kariya.

“Kowa ya bi matakan nan da aka runguma daga farko, ba sai gwamnati ta hana ka ba, ba sai gwamnati ta kafa doka sannan ka kare kanka ba.”

Likitan ya ce matakan sun haɗa da sanya takunkumi da bai wa juna tazara da wanke hannu akai-akai da kuma yawan amfani da man goge hannu na sanitaiza.

“Duk waɗannan suna rage kaifi da saurin yaɗuwar cutar a cikin ƙasashe, yanzu ne ya kamata a sake komawa ga matakan.”

Yaya sabon nau’in cutar korona yake?

Birtaniyan ce ta gano wannan sabon nau’i da bincike ya nuna ya fi saurin kama mutum da saurin yaɗuwa da kuma saurin yin ɓarna.

Dr Gwazo ya ce a yanzu an kai matakin da sabon nau’in cutar ya fara maye gurbin tsohuwar koronan don yanzu babu ita da yawa masu sabuwar sun fi yawa.

“Wannan ya nuna cewa annobar ta fara shiga yanayin da ake kira mutation, wato yanayin da ƙwayar cuta ke sauya yanayi don ta fi ƙarfi.

“Wannan ba sabuwar al’adar ƙwayoyin cututtuka ba ce, tsohuwar al’ada ce musamman ga cututtukan da ke yaduwa ta numfashi kamar irin su mura.

“Da wuya ƙwayar cutar mura ta bana ta yi kama da ta bara sannan ta baɗi ba za ta yi kama da ta bana ba, dole a samu bambanci a tsakaninsu na ƙarin kaifin yaɗuwa ko na ƙarin kaifin ɓarna,” in ji masanin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here