Batun Sabbin Kudi: Kai Abokina ne, Amma Zan sa a Kama ka – Gbajabiamila ga Emefiele

 

Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila ya yi barazanar amfani da tanadin kundin tsarin mulkin kasar nan; sashe na 89(D) don kwamushe gwamnan CBN tare da kawo shi gaban majalisar.

Sashen na 89 a kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba majalisa karfin ikon ba da umarnin kamu ga duk wanda ya gaza amsa gayyatarsa.

A jiya Laraba 25 ga watan Janairu, majalisar wakilai ta shirya zama da manyan masu ruwa da tsaki na CBN da shugabannin bankuna don jin ta bakinsu game da dalilin da yasa ake samun karancin sabbin kudade a bankunan kasar nan.

Hakazalika, zaman an ce zai yi duba ga yiwuwar sake sanya sabon wa’adi ga daina amfani da tsoffin kudade da bankin na kasa ya buga a watan jiya.

Dalilin da yasa ake neman zama da gwamnan CBN

Idan baku manta ba, majalisar kasa ta nemi Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dage wa’adinsa na 31 ga watan Janairu zuwa karshen watan Yuli don ba kowa damar rabuwa da ala-ka-kai na tsoffin kudade.

Sai dai, gwamnan bai halarta ba, kana bai turo wakili zuwa zaman da aka shirya yi a jiya Laraba da misalin karfe 3 na yamma ba, wannan yasa aka sake tura zaman zuwa ranar Alhamis.

A cikin wasikar da majalisar ta karanta a ranar Alhamis, mataimakin gwamnan CBN ya ce, Godwin Emefiele na daya daga cikin tawagar da aka tura zuwa birnin Dakar, kasar Senegal.

Kai abokina ne, amma zan sa a kama ka

Da yake martani ga CBN, Gbajabiamila ya ce, duk da cewa Emefiele abokinsa na kut-da-kut, shi da sauran mambobin majalisa na da ikon tankwara shi daidai da tanadin kundin tsarin mulki.

Ya ce gaskiya gwamnan CBN bai kyauta ba da ya gaza amsa gayyatar majalisar, kana ya ki turo wakili a irin wannan yanayi mai bukatar ujila.

Ya ce matukar ganawarsu ta gagara ga kuma ‘yan Najeriya na fuskantar wahala, zai turasasa sufeto janar na ‘yan sanda ya kamo gwamnan tare da kawo shi gaban majalisa.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here