An Nada Amb. Mustapha a Matsayin Wazirin Dambatta

Sarkin Fulanin Dambatta da ke jihar Kano, Alhaji Aminu Bello Sulaiman ya amince da naɗin Amb. Mustapha a matsayin wazirin  Dambatta.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwar naɗin da fadar Sarkin Fulanin Dambatta ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin shirye – shirye Dr. Bello Adamu Namura.

Sanarwar ta ce “Bisa dogon nazarin halayenka da kuma la’akari da gudummawarka ga Dambatta, jihar Kano da kasa baki daya, da kuma girmama masarautar Dambatta, Mai girma Sarkin Fulani-Dambatta ya umarci a sanar dakai cewa kana daya gada cikin wadanda ya amince a baka mukamin sarautar waziri a Dambatta“

“Saboda haka an tsara jadawalin shirye shirye da tsare tsaren bikin nadin, wanda da zajar an gama shirye shiryen bikin nadin sarautar, kwamitin tsare tsaren zasu sanar da kat lokacin da za’ayi bikin nadin da zarar an sa rana”

“A madadin Mai girma Sarkin Fulani, muna tayaka murnar samun warnan sarauta da kuma addu’ar Allah Ya tayaka riko, Ya zama jagora bisa wannan amana da nauyi daya dora maka. Muna kuma fatan za’a bada hadin kai wajen bin umurni da dokokin wannan masarauta”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here