Satar Mutane ya Dauƙi Sabon Salo a Najeriya
Matsalar satar mutane na daukar wani sabon salo a Najeriya, kasancewar yadda ake zuwa keɓaɓɓun wurare kamar masallaci da asibiti ana satar mutane.
A jihar Nasarawa, kamar wasu sassan kasar da matsalar ta yi ƙamari an sace wasu mutum hudu a wani asibiti a garin Lafia, bayan wasu mutum 17 da aka sace a wani masallaci a karamar hukumar Toto.
Hakan na nufin cikin mako ɗaya an sace mutum 22 a jihar.
Amma mahukunta sun ce an saki wasu daga cikin mutanen da aka sace a Masallaci, kamar yadda Gidado Fari kwamandan hukumar tsaron farar-hula da ƙadarorin gwamnati a jihar Nasarawa ya shaida wa BBC.
“An sako wasunsu bayan sun bayar da ƙudi kamar yadda suka faɗa,” in ji shi.
Satar mutane ba sabon abu ba ne a Najeriya, amma yadda matsalar ke ta’azzara, da yadda ake satar a ko`ina, ciki har da tsarkaka da keɓaɓɓun wurare, kamar masallatai da asibitoci da makarantu, ita ce sabuwar matsala da ke nuna irin munin da matsalar ta yi.
Read Also:
Ko a lokutan yaki da rigingimu, akan yafe wa waɗanda suka ruga masallatai da coci-coci da sauran wuraren ibada, da asibitoci da sauran su. Amma yadda, abubuwan da ke faruwa a yanzu na nuna cewa kusan babu wanda ya tsira daga matsalar satar mutanen.
Babban ƙalubale ne
Wannan al’amarin ya sa mutane ke jan hankalin mahukunta domin su dauki mataki ganin yadda matsalar satar mutanen domin ƙudin fansa ke neman zarta iyaka.
Masharhanta kamar Mallam Muhktar Wakil ya ce duk da jami’an tsaro na iya ƙokarinsu amma wannan babbar barazana ce ga zaman lafiyar al’umma.
Ya ce akwai jan aiki a gaban hukumomi na kawo ƙarshen matar ta satar mutane.
ko da yake a cewar kwamandan hukumar da ke kare farar-hula ta Civil Defence, Gidado Fari, Irin wannan yaki da miyagun boye, sai da haɗin kan jama’a.
“Kalubalen shi ne ba mu samun labarai daga mutane saboda ana jin tsoro, amma da za a samu haɗin kan jama’a za a kawo ƙarshen matsalar” in ji shi.
Masharhanta dai na ganin matsalar satar mutane, matsala ce da ke addabar sassan Najeriya da dama da ke bukatar dakilewa cikin gaggawa.
Bayan durkusar da jama`a da take yi sakamakon dukiyar da miyagu ke kwata da sunan kudin fansa, tana karya tattalin arzikin al`umma baki daya, sakamakon yadda ake tilasta wa manoma da sauran jama`a kaurace wa gonakai da sauran wuraren sana`arsu.