Abubuwan da ya Kamata ku Sani Game da Sabon Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da masu yi wa arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta samu sabon shugaba.
Ola Olukoyede shi ne mutum na farko wanda ya fito daga Kudancin Najeriya da zai shugabanci hukumar EFCC.
Olukoyede wanda haifaffen jihar Ekiti ne, ya riƙe muƙamai da dama a hukumar kafin ya kai ga matsayin shugaba.
FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da masu yi wa arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ne ya sanar da naɗin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Ana sa ran Olukoyede zai yi aiki na tsawon shekaru hudu, bayan majalisar dattawa ta amince da shi.
A watan Yunin wannan shekara ne dai shugaba Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC.
Read Also:
Daga nan shugaban ƙasar ya naɗa Abdulkarim Chukkol, wanda a lokacin yake riƙe da muƙamin daraktan ayyuka a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar.
Abubuwan sani dangane da Olukoyede
Ga abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon shugaban na hukumar EFCC:
Olukoyede ya fito daga jihar Ekiti, a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, shi ne mutum na farko da ya fito daga Kudancin Najeriya da zai taba riƙe shugabancin hukumar tun bayan kafa ta
An haife shi a Ikere-Ekiti a ranar 14 ga Oktoban 1969.
Ya yi karatu a jami’a a jami’ar jihar Legas (LASU), Institute of Arbitration – ICC da ke Faransa da kuma jami’ar Harvard.
Olukoyede gogaggen lauya ne wanda ke da shekaru sama da shekara 22 na ƙwarewa a fannin.
Ya na da ƙwarewa sosai a harkokin hukumar EFCC, inda a baya ya taɓa riƙe mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban hukumar (2016-2018).
Babban fasto ne a Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi sakataren hukumar EFCC (2018-2023)