‘Yan Bindiga Sun Sace ɗalibai 4 na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi

 

Jihar Nasarawa – Wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai huɗu na jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi ranar Litinin da daddare.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ‘yan bindigan sun sace ɗaliban da misalin ƙarfe 10:30 na dare lokacin da suka kai farmaki Anguwan Ka’are, ƙaramar hukumar Keffi.

Ɗaliban da maharan suka yi garkuwa da su sun haɗa da, Rahila Hanya, Josephine Gershon, Rosemary Samuel, da kuma Goodness Samuel, duk ‘yan aji ɗaya watau 100 Level.

Yayin da aka tuntuɓe shi, jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Abraham Ekpo, ya ce hukumar makaranta ta samu labarin garkuwa da ɗalibanta da ‘yan bindiga suka yi.

Ya ce jami’an tsaron cikin jami’ar jihar Nasarawa na aiki ƙafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an ceto ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

Ƙarin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com