Za’a Kafa Sabuwar Doka Kan Man Fetur a Watan Afrilu – Ministan Man Fetur
Ministan Man Fetur ya bayyana cewa za’a kafa sabuwar doka kan man fetur a watan Afrilu.
Shugaban NNPC ya yi fashin baki kan lamarin tallafin man fetur.
Yan Najeriya sun lashi takobin zanga-zanga idan aka kara farashin man fetur Shugaban kamfanin man feturin Najeria (NNPC), Mele Kyari, ya bayyana cewa kowani wata ana biyan kudin tallafin man fetur na kimanin bilyan 100 zuwa 120.
Kyari ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin hira da manema labarai a taron da kwamitin yada labaran fadar shugaban kas ata shirya, Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
Wannan ya tabbatar da cewa har yanzu gwamnatin Buhari na biyan kudin tallafn mai. A watan Mayu na shekarar 2016, farashin litan mai ya tashi daga N80 zuwa N145.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa farashin ya tashi ne saboda ta daina bada tallafin man fetur.
Amma yanzu shugaban NNPC ya ce ba zai yiwu a cigaba da sayar da litan mai fetur N162 ba.
Ya yi jawabinsa bayan karamin Ministan arzikin mai, Timipre Sylva, ya bayyana lokacin da za’a samar da sabuwar dokar kamfanin man fetur (PIB).
Kyari ya ce bayanan dake cikin takardunta sun nuna cewa N234 ya kamata a rika sayar da litan mai, amma N162 ake sayarwa.
Ya ce wajibi ne a bari tashi da saukan farashin danyan man su rika gudanar da yadda farashin litan tataccen mai zai kasance.
Ya kara da cewa kawai gwamnati ta yi tunanin irin halin da yan Najeriya zasu shiga ne idan aka wajabta musu sayan mai a farashin da ya kamata.