An yi Jana’izar Tsohon Limamin Masallacin Harami Sheikh Muhammad Ali Al-Sabani
An yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami da ke birnin Makkah, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni.
Ya kasance daya daga cikin limaman da ke jagorantar sallar Taraweeh a Masallacin Harami a watan Ramadan kimanin shekara 57 da suka gabata.
Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni ya rasu yana da shekaru 91 a duniya Rahotanni sun kawo cewa an yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami da ke birnin Makkah, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni a kasar Turkiyya.
Babban malamin, Sheikh Muhammad Ali Al-Sabuni, ya kasance daya daga cikin limaman da ke jagorantar sallar Taraweeh a Masallacin Harami a watan Ramadan kimanin shekara 57 da suka gabata.
Sheikh Al-Sabuni mai shekaru 91 ya kwanta dama a garin Yelwa a kasar Turkiyya, a ranar Juma’a, 6 ga watan Sha’aban 1442 Hijiriyya.
An haifi Sheikh Al-Sabuni ne a kasar Syria, kuma ya rubuta litittafai masu yawa a kan ilimin tafsirin Al-Kur’ani mai girma, ciki har da “Taisiru Karimur Rahman Fi Tafsiri Kalamul Mannan,” wanda aka fi sani da suna Tafsirin Sabuni.
Marigayin ya shafe kimanin shekara 28 yana koyarwa a Tsangayar Shari’ar Musulunci da ke Jami’ar Ummul Kura da kuma Tsangayar Ilimi da Tarbiyya ta Jami’ar Musulunci ta Sarki Abdul Aziz, dukkansu a birnin Makkah, jaridar Aminiya ta ruwaito.