Jami’in ‘Dan Sanda ya Bindige Abokin Aikinsa Bisa Kuskure a Jahar Abia

 

Jami’in dan sanda ya bindige abokin aikinsa bisa kuskure a garin Aba da ke jahar Abia.

Hakan ya faru ne a lokacin da yan sandan ke kokarin kama wasu da ake zargi da laifi.

Kakakin rundunar yan sandan jahar, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da hakan amma bai yi cikakken bayani ba Jami’in dan sanda a garin Aba, Jahar Abia, a jiya ya kashe wani abokin aikinsa yayin kokarin kama wani da ake zargi da aikata laifi.

Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Bata Junction, yayin da dan sandan ke kokarin harbin wanda ake zargin amma ya yi kuskure ya bindige abokin aikinsa.

Wani da abin ya faru a idonsa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan sandan sun yi kokarin tsare wata mota kirar Jeep mai bakin gilashi suka kuma kokarin tilastawa wadanda ke cikin motar su fito su shigar motarsu ta sintiri.

Wani dan sandan daban da ke cikin motar Jeep din ya yi kokarin rokon abokan aikinsa su kyalle su amma ba su amince ba.

Da mutanen da ke cikin Jeep din suka ki shiga motar yan sandan shine daya daga cikin yan sandan ya fito da bindiga ya harbi abokin aikinsa cikin kuskure a maimakon harbin wanda suke son kama wa.

cewar shaidun ganin ido, “Da dan sandan ya harbi abokin aikinsa, nan take suka kyalle wanda suke zargin suka koma kokarin taimakon abokin aikinsu.”

Dan sandan da aka harba ya rasu a hanyarsu na zuwa asibiti amma ba a iya tabbatar da hakan ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kakakin yan sandan jahar Abia, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba a masa bayani a hukumance ba don haka ba zai yi tsokaci kan lamarin ba a yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here