An Sace Motar Ofishin Mai ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu a Abuja
FCT, Abuja – Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya reshen Abuja ta kaddamar da bincike kan sace mota a masallacin Juma’a.
Rundunar ta fara farautar barayin da suka sace motar jami’in ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu a Abuja.
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ranar Juma’a 11 ga Afrilun 2025 da misalin karfe 1:05 na rana.
Ribadu ya sha alwashi kan matsalar tsaro
Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Nuhu Ribadu ya ce tsaro ya inganta da kuma fadin kokarin Gwamnatin Tarayya kan haka.
Malam Nuhu Ribadu ya fadi haka yayin kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina bisa rasuwar mahaifiyarsa.
Read Also:
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce alamu sun nuna cewa an samu raguwar matsalar tsaro a jihar Katsina.
Tsohon shugaban EFCC ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin da jihar Katsina take yi na dawo da tsaro da zaman lafiya.
Yadda aka sace motar ofishin Ribadu a masallaci
Jami’in da ke ofishin Ribadu ya ajiye motar kirar ‘Toyota Hilux’ mai launin baki a Area 10, a gaban ofishin AMAC domin halartar sallar Juma’a.
Da ya dawo daga masallaci sai ya tarar da cewa an sace motar, wanda hakan ya tayar da hankali sosai.
Majiyar ta kara da cewa an kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Garki da misalin karfe 2:00 na rana.
Hakan yasa aka hanzarta aiwatar da duba kowace mota da ke shiga da fita daga birnin domin dakile barayin.
Rundunar ta ce suna ci gaba da kokari domin kama wadanda suka aikata laifin da dawo da motar da aka sace.
Za a ci gaba da zurfafa bincike har sai an kamo wadanda ke da hannu a cikin satar motar jami’in ofishin Nuhu Ribadu.