Da Yiyuwar Za’a Kara Saka Dokar Kulle Jahar Kaduna

 

‘Yan Najeriya sun fara nuna damuwarsu dangane da hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu.

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yi kurarin cewa zai sake saka dokar kulle a fadin jiharsa.

A cewar gwamnan, zai sake saka dokar ne idan jama’a basu kiyaye ba ko kuma idan alkaluman masu kamuwa da cutar suka cigaba da hauhawa.

Mallam Nasir El-Rufa’i, gwamnan jihar Kaduna, ya ce akwai yiwuwar zai sake saka dokar kulle saboda hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona da ake samu a jihar da fadin kasa.

Abdallah Yunus Abdallah, mai taimakawa El-Rufa’i a bangaren watsa labarai, ya ce gwamnati za ta dauki wannan mataki ne saboda kare hakkin kare rayukan mutanen jihar ya rataya ne a wuyan gwamnan.

A cewarsa, gwamnan ya yi wannan jan kunnen ne saboda alhakinsa ne ya kula da lafiyar mutanen jihar Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Hadimin gwamnan ya kara da cewa babu abinda zai hana gwamnan Kaduna ya sake saka dokar kullen jama’a matukar basu kiyaye sharudan kare kai domin dakile yaduwar cutar ba ko kuma idan alkaluman masu kamuwa da cutar suka cigaba da hauhawa.

“Yaki da cutar korona aiki ne da ya rataya a wuyan dukan jama’a, ba iya gwamnati kadai ba, a saboda haka ya zama wajibi a kan mutane su kula tare da yin biyayya ga dokoki da matakan kare kai domin dakile yaduwar cutar, a cewarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here