Gwamnatin Tarayya ta ce za ta Iya Saka Dokar Ta-ɓaci a Anambra Saboda Zaɓe
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta iya saka dokar ta-ɓaci a Jahar Anambra da ke kudancin ƙasar domin tsaurara tsaro yayin gudanar da zaɓen gwamna a watan Nuwamba.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ranar Laraba wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.
Read Also:
Malami ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa domin ta tabbatar da tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu “idan gwamnatin jahar ta gaza yin hakan”.
“Idan aka samu tabbacin cewa gwamnatin jaha (Anambra) ba za ta iya kare rayukan mutane ba ta hanyar tabbatar da doka da oda gwamnatin tarayya za ta ɗauki mataki kuma za mu iya saka dokar ta-ɓaci,” a cewarsa kamar yadda Channels TV ta rawaito.
Matakin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe a Anambra da kuma yankin kudu maso gabashin Najeriya.
An kashe mutum fiye da 10 a ‘yan makonnin da suka wuce a Anambra. Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta saka 6 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaɓen gwamna a jahar.