Ana Buƙatar Sama da Dala Biliyan 50 Domin Sake Gina Gaza
An ƙiyasta cewa aikin sake gina Zirin Gaza da Gaɓar Yamma zai laƙume kuɗi sama da dala biliyan 50 kuma zai kwashe tsawon shekara 10.
Read Also:
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai da kuma Bankin Duniya ne suka yi wannan ƙiyasi.
Ƙiyasin ya nuna cewa za a buƙaci dala biliyan 20 domin aikin sake gina yankin a shekara uku na farko.
Kashi 60 cikin ɗari na gine-ginen da ke Gaza ne hare-haren Isra’ila suka lalata, lamarin da ya bar ɓaraguzai da yawansa ya kai tan miliyan 50.