An Sake Zaben Tinubu a Matsayin Shugaban ECOWAS
An sake zabar Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu a matsayin Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a wa’adi na biyu.
Tinubu wanda wa’adin mulkinsa zai kare ranar 9 ga watan Yunin 2024, an sake zaben sa ne bisa hukuncin shuwagabancin kungiyar a yayin gudanar da taron ta karo na 65 a Abuja a ranar Lahadi.
Read Also:
A yayin da yake jawabi bayan sake zaben nasa, Bola Tinubu ya ce, “Na karbi wannan mukami domin ci gaba da habaka wannan tafiya ta dimukuradiyya, kuma mu hidimtawa wannan yankin da muka gada daga hannun magabatanmu”.
Wasu rahotanni daga fadar shugaban kasa dai sun ce an sake zaben Tinubu a zango na biyu na shugabancin kungiyar ta ECOWAS domin ya ci gaba da jan ragamarta.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, waɗanda a baya suka sanar da ficewa daga ƙungiyar suka ce sam ba su da sha’awar dawowa cikinta.