Rashin Lafiya: An Saki ɗaruruwan Fursunoni Daga Gidan Yarin DR Congo
An saki fursunoni 1,685 masu fama da rashin lafiya daga gidan yarin Makala da ke Kinsasha, babban birnin ƙasar Dimokuraɗiyyar Jamhuriyar Congo domin rage cunkoso.
Read Also:
A gidan yarin ne a farkon wannan watan na Satumba fursunoni 129 suka mutu bayan sun yi yunƙurin tserewa. Jami’an tsaron gidan ne suka harbe wasu, wasu kuma suka mutu a turmutsutsu, kamar yadda mahukunta gidan yarin suka bayyana.
Gwamnatin ƙasar ta ƙuduri aniyar aiwatar da rage cunkuson gidajen yarin cikin sauri.
Gidan yarin wanda aka gina domin fursunoni 1,500 a shekarun 1950, kafin yunƙurin tserewa da aka yi a wannan watan, fursunoni 12,000 ne a ciki.
Wani tsohon fursuna da ya taɓa zama a gidan yarin ya shaida wa BBC cewa, “Makala ba gidan yari ba ne, wajen tsare mutane, inda ake tura su domin su mutu,” in ji shi.