Mun Sako da Kudin Data – Dr Isah Pantami
Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis tace an rage kudin ‘Data’ da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC.
Saboda haka, kudin ‘Data’ na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu ( tun watan Nuwamba), The Nation ta ruwaito.
‘Data’ kudi ne da mutum ke saya a domin amfani da samun shiga yanar gizo.
Read Also:
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka baiwa hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin ‘data’ a fadin tarayya.
“Farashin kudin Data ya sauko daga N1000 da ake sayarwa a Junairu 2020, zuwa N487.18 fari daga watan Nuwamba, 2020,” Hadimin Pantami, Femi Adeluyi yace.
“Haka yake kunshe cikin rahoton da hukumar sadarwan Najeriya NCC ta aikewa Minista bisa umurnin da ya bayar.”