Abubuwa Game da Sakonnin da yake Yaɗawa Akan Manhajar WhatsApp 
A kwanan nan duk mai amfani da dandalin sada zumunta na Whatsapp to ya gamu da ɗaya daga cikin waɗannan sakonnin da zami bayani a kai.
 Mutane na ta kokarin turawa abokanan su sakonnin duk da cewa basu da hujjar kare kansu cewa dokokin daga WhatsApp suke.
 A wannan rubutun mun tattara muku dukkanin waɗannan jita-jita da ake yaɗawa tare da bayani mai gamsarwa kan gaskiyar lamarin.
Abuja – Duk mai bibiyar kafafen sada zumunta na Facebook, Instagram da WhatsApp, ya san cewa makon da ya gabata bai zo wa mamallakinsu, Mark Zuckerberg, da daɗi ba.
 Ya rasa dala biliyan $5.9bn wanda a jimlace yakai dala biliyan $117bn a makon da ya gabata saboda matsin lambar da yake fama da ita a ɓangaren gudanarwa da kuma ɗaukewar manhajojin kamfaninsa.
A rahoton dailytrust, lamarin ya shafi yardar da masu zuba hannun jari suka wa kamfanin, inda suka rage kusan kashi 4.8% kuma suka kwashe makudan kudi daga dukiyarsa.
Dandalin Facebook kaɗai ya samu matsaloli biyu; ɗaukewar da ya yi tare da ƙawayensa Instagram da WhatsApp, abinda ya jawo asarar miliyoyin daloli.
Damuwa ta biyu kuma itace babban taron da tsohuwar manajan Facebook, Frances Haugen, ta yi ranar Talata bayan ta ɗauki matakin murabus da kuma fallasa wasu bayanai.
Haugen ta caccaki Facebook bisa , “Fifita ribar da zai samu kan mutane,” da kuma gazawa wajen tsare bayanai bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2020 a Amurka.
Sakonnin da ake yaɗawa a WhatsApp
Duk wannan abubuwan ba su kare ba, a halin yanzun dandalin WhatsApp ke fama da yaudara kala daban-daban.
Wasu daga cikin waɗannan yaudara da kuma damfara wauta ce kawai, amma wasu kuma sun jefa masu amfani da shafin cikin tantama.
 Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin waɗannan jita-jitar da ake yaɗawa na yaudara, waɗanda zaku kiyaye:
1. Za’a rufe WahtsApp da karfe 6:00 na yamma
 Abu na farko daga cikin jerangiyar sakonnin da mutane ke yaɗawa a Whatsapp shine kamar haka:
 “Gobe da misalin ƙarfe 6:00 na yamma zasu garƙame manhajar WhatsApp kuma saika biya zaka ƙara amfani da shi, wannan doka ce.”
 “Muna sanar da duk masu amfani da manhajar mu, mun samu matsalan Na’ura, muna son ku taimake mu wajen isar da wannan sakon ga kowa da kowa.
Idan baka tura wannan sakon ga dukkan abokanka ba to zamu fara cajin ka kuɗaɗe.”
“Zamu rufe shafinka kuma zaka iya rasa dukkan abokanan ka, sako daga Jim Balsamic (shugaban WhatsApp). Muna bukatar kowa ya tura wannan sakon, idan ba haka ba zamu rufe shafinka cikin awanni 48.”
Sakon ya cigaba da cewa idan muka rufe maka shafi to zamu ƙara dala £25 a kuɗin da zaka rinka biya duk wata. “Muna sane da matsalar da kuke fuskanta wajen canza hoto, muna aiki ba dare ba rana domin warware matsalar, kuma zamu gyara ta cikin kankanin lokaci. Mungode da haɗin kan da kuke bamu, daga Whatsapp.”
Jita-jitar ta nuna cewa wai WhatsApp zai fara cajin mutane kudi saboda mutane sun yi musu yawa, babu ta hanyar da wannan maganar zata zama gaskiya WhatsApp yace ba zai goge shafin mutun ba dan kawai mutane sun yiwa manhajar yawa kuma ba tare da izinin mutum ba.
2. Daftarin biyan kudin manhajar WhatsApp
Bamu sani ba ko ka taba samun gayyata daga wani? idan ma sakon bai isa gareka ba, tuni wasu suka fara tura daftarin Gold ga masu amfani da dandalin.
Abinda ya kamata kusani WhatsApp ba zai taɓa tura sakonnin gayyata na Pro, Gold, Plus, Star ko wani daftari na daban ba tare da ya fitar da sanarwa ba.
3. Cutar WhatsApp (WhatsApp Biros)
 Ita kuma wannan cutar bata zuwa wa mutun kai tsaye daga WhatsApp, sai dai ta hanyar sakon Email a wayar salula.
Wasu na tura wa mutanen dake amfani da dandalin WhatsApp saƙon Email ɗauke da adireshin yanar gizo-gizo, sakon na cewa an tura maka sakon murya ko kiran murya a shafinka.
Da zaran mutum ya taba wannan adireshin yanar gizo dake kunshe a sakon nan take cutar zata shiga wayarsa kai tsaye. Kai tsaye zamu iya cewa wannan ƙarya ce domin WhatsApp bai taba sakin sanarwa daga wani wuri da yake ba wajensa ba.
 Babu dalilin da WhatsApp zai sanar da mutum wani abu ta hanyar amfani da abinda basu da alaƙa kamar sakon Email, zai fi kyau mutum ya yi watsi da irin wannan.
4. Jerin muhimman sakonni daga WhatsApp Tabbas kusan kowa ya samu irin waɗannan sakonni, inda ake umartarka da ka tura wa mutum 10 dake cikin lambobin wayarka.
Babu tantama waɗannan sakonnin karya ce tsagwaronta, muna baka shawara ka yi watsi da irin waɗannan bayanan.
Misalin irin wannan sakonnin da ake yaɗawa shine:
 “Barka! nine DAVID D. SURETECH, wanda ya ƙirƙiri Whatsapp. Muna sanar da masu amfani da manhajar mu cewa muna da sabon shafi miliyan 53m ne kacal, waɗanda mutane zasu iya buɗewa sabo.”
 “Mutane sun mana yawa, muna bukatar taimakon ku wajen warware wannan matsalar. Muna son duk waɗanda ke amfani da mu a yanzun su tura wannan sakon zuwa ga dukkan abokansu.”
 “Ta haka ne kaɗai zamu gane ainihin masu amfani da WhatsApp da wanda suka daina amfani da shi… sakon ya cigaba har zuwa ƙarshe.”
Game da wannan, kamfanin WhatsApp ya yi martani da kansa:
 “Babu wasu kuɗaɗe da WhatsApp zai caji masu amfani da shi, muna san ku fahimci cewa wannan jita-jita ce da bata da tushe ballantana makama.”
5. Manhajar WhatsApp Spy
Da yuwuwar ka samu sakon sabuwar manhajar WhatsApp Spy , wadda zata baka damar shiga ka karanta abubuwan da wasu ke aikata wa a shafinsu.
 A zahirin gaskiya wannan ƙarya ce tsagwaronta kuma ku ɗauki lamarin a matsayin soki burutsu ne kawai. Bayan kammala jin irin waɗannan labarai da mutane ke yaɗawa, Legit.ng ta nemo muku ingantaccen bayani daga kamfanin WhatsApp.
“Muna aiki da dukkanin karfinmu wajen rage saƙonnin karerayi dake shiga na’urar mu. Zami ƙirƙiri wuri da zai bada fifiko ga maganar da mutane ke yi da yan uwansu…”
 “Matukar an turo maka irin wanna sakon to muna baka shawara ka datse ma’amala da wanda ya turo maka shi kuma ka goge sakon.”
“Domin guje wa cutar da abokanka, kada ka kuskura ka tura wa wani wannan sakon, ka gagguta kai rahoton shi sashin Spam.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here